An zaɓi sabon shugaban Jam’iyyar APC na Arewa a Jihar Legas

Daga JAMIL GULMA

Rahotanni daga birnin Legas suna nuni da cewa an zaɓi sabon shugaban jam’iyyar APC na Arewa a Jihar Legas.

An dai zaɓi Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Arewa mazauna Legas.

Zaɓen ya biyo bayan neman canjin da al’ummar arewa da ke zama birnin na Ikkon suka daɗe suna nema sanadiyyar rashin kawo ci gaba ta fannoni daban-daban.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ofishin sa bayan kammala zaɓen, sabon shugaban ya gode wa Allah bisa ga wannan matsayin da Allah ya ba shi ya kuma yaba wa tsohon shugaba Alhaji Dandamma Yabo bisa ga tunanin sa wajen zaƙulo shi duk da ya ke ba shi kaɗai ne ya nemi wannan kujerar ba amma ya nemi ba sai an kai ga aiwatar da zaɓe ba, saboda yin haka shi ne zai tabbatar wa idon duniya kan ‘yan arewa mazauna Legas a haɗe ya ke.

Ya kuma sha alwashin tafiya tare da kowa saboda kowa ya zo da irin hikimar da Allah ya huwace masa Don  a gudu tare a tsira tare tare da samun romon dimokuradiyya.

Alhaji Madu Shugaban Matasa a babbar mayankar Legas (Abbatuwa) ya bayyana jindadinsa bisa ga wannan canjin da aka samu kuma cikin ikon Allah sai aka sami mutum haziƙi wanda kowa ke zaton za a sami nasarori a cikin jagorancinsa.

Dalilin goyon bayan Alhaji Sa’adu shi ne ka san wa ke jagorantar ka da kuma a ina zai kai ka, duk wani ɗan Arewa in dai mazauni Legas ne ya san ko wane ne Alhaji Sa’adu kuma ya San me ya ke iyawa.

Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma

Kamar yadda kuma duk wani mazauni Legas ya sani, al’ummar Arewa an bar su baya da nisa wajen cin gajiyar  dimokuradiyya saboda wadansu dalilai duk da ya ke idan ka cire yarbawa ba wata al’umma da ta fi arewa bayarda gudummawa ta kowane ɓangare a Jihar ta Legas musamman a siyasance.

Shugaban ƙungiyar direbobi sashen manyan motoci Muhammadu Auwal ya nuna damuwarsa bisa ga rashin takamaiman matsuguni inda al’ummar Arewa ke gudanar da lamuransu tun kama daga siyasa zuwa karɓar baki da sauran muhimman abubuwa inda ya nemi sabon shugaban da ya saka wannan kudurin a cikin ayyukan da zai soma da su. Ya kuma bayarda tabbacin ci gaba da goyon baya ta inda duk aka nema.