Yadda ‘yan bindiga suka addabi garuruwan ƙaramar Hukumar Kurfi a Katsina

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Nisan ƙaramar Hukumar Kurfi da garin Katsina bai kai kilomita 40. Amma kakaf ɗin gaguruwan da ke cikin ƙaramar hukumar, zai yi wahala a samu wanda ‘yan bindiga ba su shiga sun kwashi dabbobi ko dabbobi da mutane, ko kuma duka biyun ba.

Kamar sauran ƙananan hukumomin Katsina da ‘yan bindiga suka addaba, ita ma ƙaramar Hukumar Kurfi ta daɗe ta na fama da wannan gagarimar matsala.

Matakan tsaron da ake ɗauka a cikin Kurfi ya sa ‘yan bindiga na kewayewa ba su shiga cikin garin, sai dai su shiga sauran ƙauyukan da ke kusa da garin su yi ɓarnar da suka ga dama, su yi gaba.

To amma baya-bayan nan, ‘yan bindiga sun shiga cikin Kurfi, sun yi garkuwa da mutane, sun arce da su.

A farkon watan Agusta, Sani Mairariya ya yi nufin tafiya gonar sa da sassafe, wadda ke yamma da garin Kurfi. Abin ka da tsautsayi, a ranar, sai wani maƙaucinsa ya ce zai raka shi, kuma zai ɗauke shi kan babur, su je su gano masarar da Mairariya ya shuka.

Sun fita tun ƙarfe 8 na safe. Sai dai sun yi rashin sa’a ‘yan bindiga sun kama su a cikin gonar, inda nan take an fara nausawa da su sai aka bindige abokin tafiyarsa.

‘Yan bindiga sun bindige Mairariya bayan sun ɗan ƙara matsawa gaba kaɗan, kuma suka ƙwaƙule aljihunsa, suka tafi da wayarsa.

Abokinsa da aka fara harbewa aka yi gaba, ya taƙarƙare ya kira ‘yan uwan Sani Mairariya, ya shaida masu cewa an harbe shi, amma an yi gaba da Sani. Bayan ya yi wannan bayani ne ya rasu.

Bayan an ɗauko gawarsa, ba a tsanan ta neman Sani Mairariya a cikin dajin ba, saboda ana tunanin an yi garkuwa da shi.

Daga baya an kira wayarsa, inda maharan suka nemi a biya su Naira miliyan 3 kafin su sake shi. Wato ba su faɗa wa danginsa cewa shi ma sun harbe shi ba.

Matsalolin rayuwa na yau da kullum sun sa an kasa haɗa kuɗin, har sai bayan kwanaki 33, sannan aka haɗa Naira miliyan 2 da dubu 600. An je an kai kuɗin ne bisa hanyar komawa gida a ciki Naira 400,000, sai, mai kai kuɗi ya biya ta gonar da aka kama su Sani. Ai kuwa sai ya yi arba da gawar sa, lokacin ya kai kwanaki 33 kenan da kashewa.

Haka ya garzaya gida ya sanar, aka je aka kwaso gawar a cikin buhu, aka yi masa jana’iza a cikin Kurfi.

Ranar Talata, 20 ga Agusta, dafifin mahara sun shiga ‘Yardanya da Wanzamai, kuma sun jidi dabbobinsu.

A ranar Laraba washegari da dare kenan, maharan sun afka wa garin Barkiya, inda suka shiga kisan rabin gidajen garin. Premium Timesy ta tabbatar da cewa an sace shanu za su kai 48, kuma an kwashi mutane. Majiya ta tabbatar da cewa wasu sun gudu a cikin dare lokacin da aka nausa cikin daji da su.

“Amma kuma wasu sun tsere, kuma shanu 11 sun koma gida da kan su,” inji wani ɗan cikin garin da ya nemi a sakaya sunansa.

“Sai dai kuma wakilinmu ya samu tabbacin cewa wani mai suna Rabi’u Tukur da aka yi garkuwa da matarsa, ya je ya kai kuɗin fansa, ya karɓi matar sa.

“Amma shi ɗan gidan Abu Mashi da aka tafi da shi, sai da aka yi tafiya mai nisan gaske a cikin dare, har gaba da Unmadau, sannan ya sulale cikin duhun amfanin gona. Ya shiga cikin wani gida a daji, da ya yi masu bayani, shi ne da safe suka kai shi Dutsinma ofishin DPO, su kuma suka kira mutanen Barkiya, aka je aka karɓo shi,” cewar majiyar mu.

Washegarin daren da mahara suka shiga Barkiya, sun koma kusa da Barkiya ɗin, suka shiga Sabongarin Rawayau da Babban Gida.

A ranar Juma’a kuma sun shiga ƙauyen Koza da yamma ƙiri-ƙiri, kuma suka shiga Salihawa, inda har suka kashe mutum ɗaya.

Ranar Asabar ‘yan bindiga sun shiga garin Birchi da Baniyo. Sai kuma ranar Lahadi suka tsallake ƙaramar Hukumar Kurfi, suka tare hanya tsakanin Tsanni da Katsina, kan titin Katsina zuwa Dutsinma zuwa ƙanƙara.

A ranar Litinin mahara sun shiga ƙauyen Nasarawa, kuma suka sake shiga ‘Yardanya. Sai Talata kuma suka shiga ɗanmarke, kusa da Barkiya, tazara kaɗan da Kurfi.

Ranar Laraba sun sake komawa Baniyo. Daga nan aka ɗan kwana biyu kuma suka afka wa ƙauyen ɗangabaci da kusa da Rawayau, a ranar 9 ga Satumba, 2024.

ƙaramar Hukumar Kurfi ta yi iyaka da ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Dutsinma da kuma Charanci. Garuruwan da ke Kudu maso Yamma da Arewa maso Yamma da Kurfi duk an daɗe ana ragargazar su.

ƙauyuka irin su ‘Yarranda, Daɗawa, Sauyawa, ƙarare, Tamawa, ‘Yarbulkara, ɗanfegi ƙaguwa, Kaware, Fadumawa, Bahirawa da Bauje, ƙauyen da ke daf da garin Kurfi, duk sun sha azabar farmakin ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Kurfi.

Haka su ma ƙauyukan ‘Yarliya’u, ‘Yarbarza da Sabon Layi kusa da Kurfi duk ba su tsira ba a hare-haren ‘yan bindiga tsawon shekaru.

“Mu babban abin da ke damun mu shi ne yadda garuruwa sama da goma idan ‘yan bindiga za su shiga, to sai sun tsallaka kwaltar Kurfi tukunna. Amma har a yi fashi a gama ba za a kawo ɗauki ba, sai bayan an yi wa mutanen ƙarƙaf sannan za ka ga jami’an tsaro sun je a sukwane.

Shekaru uku da suka gabata ‘yan bindiga sun shiga cikin Barkiya, suka tafi da Dagacin Barkiya, Ibrahim Abdullahi. Ibrahim yaya ne ga Sanatan Katsina ta Tsakiya a lokacin, Kabir Abdullahi.

Sai dai wannan karo jami’an tsaro da mutane ƙauyuka sun yi ta-maza, an bi ‘yan bindiga cikin daji an yi fito-na-fito, inda suka tsere suka bar dagacin, jami’an tsaro suka ceto shi.

By ukarofi