Yadda ‘yan bindiga suka sace ɗalibai 8 a Kaduna

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar cewar an sace wasu ɗaliban jihar su takwas tare da wasu mazauna yankin.

Gwamnatin ta ce ɗaliban da lamarin ya shafa ba a harabar makaranta aka sace su ba.

A ranar Litinin ‘yan bindiga suka sace mutum 10 a Sakandaren Gwamnati da ke Awon a yankin Ƙaramar Hukumar Kachia a jihar.

Wannan shi ne hari na baya-bayan da ‘yan bindiga suka kai a jihar duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar tare da hukumomin tsaro ke yi wajen daƙile matsalar tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan, ta ce ta gano ɗaliban da lamarin ya shafa ba a cikin makaranta aka yi garkuwa da su ba.

Ta ce hakan ya auku ne a lokacin da ɗaliban ke kan hanyarsu ta komawa gida inda ‘yan bindigar suka sace su tare da wausu mutane.

Tuni dai Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya yi tir da lamarin tare da bayyana shi a matsayin abin takaici.

Gwamnan ya ce ya samu bayyanai kan tabbacin za a ceto ɗaliban su takwas da sauran waɗanda lamarin ya shafa nan ba da daɗewa ba.