Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ana fargabar wasu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da mutum 32 ciki har da ƙananan yara tare da kashe mutum 1 a wani hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke ƙaramar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Harin na zuwa ne bayan wani makamancinsa da ‘yan bindiga suka kai a watan da ya gabata, inda ake zargin sun sace mutum 85 a garin Kabari da ke makwabtaka da garin na Kadagen Kauru, bayan ga jerin hare-hare da suka kai wasu daga cikin ƙauyukan yankin.
Bayanai sun tabbatar da cewa ana ci gaba da alhinin sace mutanen da ‘yan bindigan suka yi a ranar Litinin a garin.
Wani mazaunin garin da ya buƙaci a sakaye sunansa, ya yi wa Blueprint Manhaja ƙarin bayani a kan halin da ake ciki:
”Waɗannan mutane sun kawo hari a garin Kadage Kauru misalin ƙarfe 12:30 na dare kuma sun ɗauke mutane 32, daga ciki akwai iyalan mutum 1 wanda suka ɗaukar mishi matanshi 4 da ‘ya’yan shi guda 8.
”Kadage Kauru kawai sun ɗauki mutum 38 kuma har suka kashe wani bawan Allah guda 1.
”Daga cikin waɗanda suka sace har da na goye da mata masu ciki. Akwai kuma mutum 2 da suka ji rauni aka kai su asibiti, amma sun samu sauki har sun koma gidajensu,” inji shi.
Mutumin ya yi ƙarin bayani da cewa su a nasu ɓangaren suna iya ƙoƙarinsu, domin ‘yan ƙungiyarsu ta sa-kai da jami’an tsaro da ke sintiri a waɗannan yankuna suna iya yinsu.
Amma ya ce abin ya fi ƙarfinsu, ”domin idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Yanu dai muna zama ne na cikin tashin hankali.”
Ya yi kira ga hukumomi kama daga na ƙaramar hukuma zuwa na jiha da na tarayya da su yi duk abin da za su iya don ganin karamar hukumar ta Kauru da jihar Kaduna da ma kasar bakiɗaya sun zauna lafiya.
”Muna kira ga duk wanda yake da abin da zai iya yi don ganin an zauna da waɗannan mutane a tattauna game da lamarin nan.
”A yau idan kana ƙaramar hukumar Kauru tashin hankali da muke gani ya wuce tunanin mai tunani.
”Kullum, ranar duniya tun daga wayewar gari har dare har kusan a ce maka kwana mutane ne suke tashi. Ina mai tabbatar maka a jihohin arewacin Nijeriya in Allah ya yarda jihohin da babu ‘yan gudun hijira da suka fito daga karamar hukumar Kauru ba su da yawa.”
A wani taƙaitacen jawabi da Shugaban ƙaramar Hukumar ta Kauru ya yi wa BBC ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan ya ce suna daukar mataki kan lamarin.
Mun tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Mansir Hassan, ya ce zai bincika lamarin, to amma har zuwa wani lokaci ba amo ba labarinsa.
Jihar Kaduna dai da ke yankin arewa maso yammacin Nijeriya ta jima tana fama da matsalar tsaro.
Ko a farkon watan nan na Janairun 2026, ‘yan bindiga sun sace mutum 7 tare da halaka mutum ɗaya a ƙauyen Ningi Karku da ke jihar, bayan makamancin harin da suka kai unguwar Kabari da ke ƙauyen Gobirawa, tare da yin awon-gaba da mutum 53 da kuma halaka mutum 4.
