Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Hana Safarar mutane na ƙasa NAPTIP a ranar Talata ta bayyana cewa jami’an ta sun ceto wasu yara 58 daga cikin 300 ɗin da suka ɓace a jihar Benuwe
Shugaban shiyyar Hukumar dake jihar Benuwe Gloria Bai ta sanar da haka a taron da ta yi da manema labarai a garin Makurdi.
Gloria wace shugaban ayyukka na Hukumar Yusuf Abdul ya wakilce ta a taron ya ce Hukumar ta ceto wadannan yara a lotukata daban-daban.
Ta ce tun bayan ɓacewar yaran Hukumar a watan Mayu 2025 ta fara gudanar da bincike.
Gloria ta ce an ceto yaran a ƙauyukan Yelewata, Ukpam da Daudu dake ƙaramar Hukumar Guma.
Ta ce yaran na daga shekaru 2 zuwa 8 sannan jami’an hukumar sun kama wani Archbong shugaban waɗanda ke tsare da yaran tare da wasu mutane huɗu da suke tare da yaran.
Hukumar na tsare da waɗannan mutane domin ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran yaran.
“Tun dama can yara 300 masu shekaru 2 zuwa 8 ne suka bace inda muka iya gano 20 daga cikin su a ƙaramar Hukumar Guma dake jihar Benuwe, jihar Nasarawa da Babban Birnin Tarayya Abuja wanda har an mai da su gida wurin iyayen su.
Gloria ta ce jami’an Hukumar sun ƙara gano wasu yara shida a gidajen marayu uku a Abuja da suma an haɗa su da iyayensu.
