Yadda ‘yar shekara 19 ta kashe kanta sakamakon samun ƙarancin maki a jarrabawar JAMB

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Opesusi Faith Timilehin, ‘yar shekara 19 ta ci shinkafar ɓera a ranar Litinin saboda samun maki 190 a sakamakon jarrabawar JAMB da aka saki kwanan nan, inda makin ya gaza wanda ake buƙata a fannin da ta nema.

Timilehin, ‘yar asalin Abeokuta ce, tana zaune a Odogunyan da ke Ikorodu, Jihar Legas tare da yayarta.

Jaridar The Guardian ta samu labari cewa maƙwabta da mazauna unguwar sun shiga alhini sosai bisa mutuwar Timilehin, wadda suka bayyana a matsayin “mai hankali da biyayya.”

Wani daga cikin danginta ya ce marigayiyar ta nemi karatu a Microbiology, kuma ta sake wannan jarrabawar ne karo na biyu bayan ta zauna a shekarar da ta gabata.

“Ta ce sakamakon bara ya fi na bana kyau,” inji wata abokiyar zamanta (wanda ba a bayyana sunanta ba).

Bisa bayanai da aka samu, maƙwabta sun fara zargin wani abu da bai dace ba lokacin da Timilehin ta je ofishin yayarta tana neman (man ja) don rage azabar ciwon ciki da take ji bayan ta sha gubar a gida.

Yayarta, wadda a farko bata fahimci abin da ke faruwa ba, ta yi watsi da ita, sai daga baya ta fara ihu tana neman taimako, wanda hakan ya jawo hankalin jama’a zuwa wurin.

Rahotanni sun ce ta samu maki fiye da 190 a sakamakon JAMB na shekarar 2024.

By ukarofi