Yadda za a kawar da tabon fata (2)

*Me ke kawo tabon fata

Daga AISHA ASAS

A baya mun fara shimfiɗa ne kan ma’ana ta tabon fata, dalilin samuwar shi da kuma mahaifar shi. Mun yi wannan bayyani ne don tafiya bisa ga fahimta ɗaya, wanda hakan zai sa mu fahimci inda muka dosa a yanzu.

A wannan sati kamar yadda muka faɗa a sama, za mu yi bayyani kan ababen da ke zama silar samuwar tabon fuska, ma’ana matsalolin da ke samuwa kafin wannan sinadarin ya yi gudun kawo ceto ga fata wanda ke zama sanadiyyar barin tabo a wurin.

Akwai matsalolin fata da dama da ke zama sanadiyyar samuwar wannan tabon fuska, don haka za mu kawo wasu daga ciki kuma jiga-jigai ko in ce waɗanda suka fi zama ruwan dare.

Hasken rana:

Bazan manta ba lokuta da dama wannan shafin na kwalliya ya yi magana kan illar rana ga fatar ɗan Adam, inda muka yi bayyanin irin ranar da jiki ke buƙata, wato kafin ta yi ƙarfi, daga vulowar ta zuwa tara na safe, wani sa’ilin ma kafin tara, wannan na da alaƙa da yanayin da muke ciki, sanyi da zafi.

Lokutan zafi rana na saurin girma, don haka tana saurin kaifi da zai illata fata, saboda haka a irin wannan lokacin ko da tara za ta yi ta gama yada zango.

Wannan ne dalilin da ya sa a lokacin zafi jikin mutane musamman fuska ke zama kala biyu, saboda rana da ke bugun wurin ya fi yawa a fuska ne saboda ta fi rashin kariya, kasancewar jiki na sanye da tufafi ko in ce wani ɓangare na jiki. Wannan na ɗaya daga cikin amfanin sanya hijabi a lokacin zafi fiye da lokacin sanyi.

Duk da cewa mutanen da ba sa son shiga ta hijabi sun mayar da shi suturar lokacin sanyi, don samun kariya daga sanyin.

Sai dai hijabi duk da ana ganin shi abin da ke ƙara zafi hanyace ta ba wa fata kariya daga hasken rana, hakan ne ya sa masu yawan sa hijabi da kuma niƙabi ba a cika ganin ƙunar rana a tare da su ba, saboda sun sanya shamaki tsakanin su da ranar.

Baya ga haka za ki iya amfani da wasu daga cikin mayuka da ke bada kariya daga hasken rana, waɗannan mayukan na da yawa, abin da kawai kike buƙata shi ne, neman wanda ya dace da ta ki fatar.

Ita wannan ƙunar fata ba wai tana samuwa ne sau ɗaya ba, ma’ana ba da kinga duhu a fata na ƙunar rana ba shikenan ranar ba za ta ƙara yi ta kan wurin ba ko da kin sake shiga cikin ta ba, rana na iya dukan muhalli guda ba adadi, matuƙar ba za ki daina kai fatarki a wurin ta ba, ita kuma baza ta gajiya wurin ƙara illa kan illar da ta yi wa wurin ba.

Hakan na nufin ƙunar rana na ƙaruwa daidai da jimawar da mai ita ya yi yana tu’amali da ita, hakan zai sa a kullum wurin zai ta ƙara duhu, kuma hakan ƙarin matsala ce ga mai ita, domin matsalar za ta iya tuma ta koma wani matakin.