Dandalin shawara: Game da matsalar warin baki

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Aisha an yini lahiya. Allah Shi taimaka, Ya yi ma ki jagora. To ni ma dai da ‘yar neman shawara na taho kamar yadda aka saba yi. Wallahi miji a gare ni da yake warin jiki, babu ma kamar baki nai. Bai son yin wanka. In ya matso ni kamar in yi amai. Shi ya sa duk da Ina son auratayya wallahi har ban sha’awarta, don da ya matso sai warin ya sa abin ya fita ga raina. Kuma matsalar mijin nau na cikin irin hitinannun mazan nan ne da ba su amsar laihi idan an ce sun yi. Ko kan gaskiya kike sai sun maido mi ki laihi. Ga jinini da yawan mita. Don Allah ya kike ganin za a yi kan wagga matsala, don ta isheni. Na gode. ‘yar’uwarki…………….

AMSA:

lafiya ƙalau ‘yar’uwa. Amin. Na gode. Da farko matsalarki idan na fahimta kina tare da ƙazamin miji kuma kina tsoron sanar da shi yana wari don gudun fitinar shi, kuma hakan na cutar da ke.

Wannan matsala ce mai matuƙar cutarwa, domin masana sun tabbatar wari na ɗaya daga cikin ababen da ke iya kawar da sha’awa, kuma maza da yawa suna da wannan hali na ko-in-kula akan abin da ya shafi burge matansu ko yin abin da matan za su samu natsuwa da su a yayin kwanciyar aure.

A ta su wautar, su ne matan ya kamata su yi wa shiri yayin tarayya, kuma su ya kamata matan su tabbar sun samu natsuwa, wannan ne zai sa su je wa matansu ba tare da tsaftace jiki ba, wani ma sai ya gama kusantar iyalinshi ne zai yi wanka daga dauɗar da ya kwaso daga aiki ko kasuwa, wai a lokacin yake buqatar yin wanka don ya ji daɗin barci, sai ya haɗa da na tsarki. Amma ko kaɗan yadda matar zata ji ba abin da ya dame su ba ne.

Ina kuke ne maza masu wannan hali, ku matso da ku na ke, ina lokacin da kake tsunduma tunanin me ka yi wa matarka ta tsane ka?

Ina lokacin da kuke matakin matanku da ke gudun shimfiɗarku ba gaira ba dalili? Ina lokacin da kuke hango burgewa a idanuwan matanku a lokacin da suke kallon wani namiji a talabijin? Ina lokacin da matanku ke nuna ma ku ‘ya’yanku sun fara girma a haƙura da yawan kevewa?

Ina lokacin da kuke al’ajabin yadda matanku suka daina neman yin tarayya da ku kamar yadda suka saba? Ina lokacin da kuke tunanin dalilin da ya sa matanku ke ma ku kalon hadarin kaji ba tare da kun yi masu laifi ba? Duk waɗannan tambayoyi rashin damuwa da yadda matanku za su same ku a kwanciyar aure na iya amsa su, ko amsa wasu daga ciki.

Mata musamman matan hausawa na da kunya da kawaici musamman akan abin da ya shafi buƙata da ra’ayi a duniyar auratayya, hakan zai sa ko suna cutuwa su daure tare da shanyewa. Sai dai hakan ba yana nufin jikinsu ya haƙura ba.

Yadda ka san kana son idan ka kusanto matarka ka ji tana ɗan ƙamshi ko ka ji ba wari a jikinta, haka ita ma ta ke buƙatar hakan don ba wa sha’awararta dama ta samu yadda ta ke so. Yadda kake buƙatar matarka ta san yadda zata saraffa ka don samun gamsu, haka ita ma ta ke buƙatar hakan.

Wani lokacin ma ta fi ka buƙatar hakan kamar yadda masana suka ce, kaso mai yawa na mata jima’i kawai ba ya kawo masu gamsuwar da jikinsu ke buƙata, shi kuwa namiji zai iya samun haka.

Yana da kyau maza ku gane cewa, addini da ya ɗora wasu haƙoƙƙin mata akan ku yayin da kuka aure su har da samar masu natsuwa a tarayya ta aure, hakan na nufin kula da abin da zai iya kwantar masu da hankali a lokacin da kuka kusanto su.

Akwai ayya a cikin littafi mai tsarki da ta ce, “suna da kwatankwacin abin da kuke da shi kansu na daga kyautatawa.” Wannan na nufin duk wani abu da za ka so samu don kyautata ma, ita ma tana da haƙƙin ka yi mata shi. Shi ya sa yake sunna ga maza yin ‘yar kwaskwarima da zata ba su kuzarin gamsar da iyalansu.

Sau da yawa matanku da sauran ƙurciyarsu kuke mayar da su tsofaffi, saboda kun kashe mu su sha’awarsu tun shekaru ba su kai ba, sai kaga mace tun ba a kai ko’ina ba ta daina barci ɗakin miji, idan kuwa ta kama ayi wani abu, za a yi bisa dole, kunga sai a haifi ‘ya’ya dolaye.

Za mu ci gaba