Da sanina CBN zai sauya tsarin Naira – Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce da saninsa Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai canza tsarin wasu takardun Naira.

Buhari ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ‘yan jarida Halilu Ahmed Getso da Kamaluddeen Sani Shawai suka yi da shi a ranar Lahadi a Abuja.

Da yake amsa tambayoyi, Buhari ya ce ya gamsu kuma yana da yaƙinin ƙasa za ta amfana da sauyin tsarin kuɗin da CBN ya ƙudiri aniyar aiwatarwa.

Ya ce dalilan da CBN ya gabatar masa dangane da sauyin tsarin kuɗin, sun gamsar da shi cewa, lallai tattalin arzikin ƙasa zai amfana da hakan.

Ya ƙara da cewa, sanarwa wata ukun da CBN ya bayar kafin aiwatar da canjin bai yi kaɗan ba.

Ya ce wa’adin ya ishi kowane ɗan ƙasa sarrafa kuɗaɗensa muddin kuɗaɗen na halal ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *