Yau Buhari zai gana da shugabannin tsaro

Daga BASHIR ISAH

Yau Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da shugabannin tsaro a Abuja don tattauna batutuwan da suka shafi tsaron ƙasa.

Yayin ganawar, Shugaba Buhari zai karɓi bayanai daga jagororin tsaron kana ya yi tsokaci a ɓangarorin da ke buƙatar a bai wa muhimmanci.

Tun farko, a wannan Litinin ɗin aka shirya a kan Buhari zai ƙaddamar da cibiyar kimiyya da fasaha ta NASENI amma sai aka ɗage sakamakon taron gaggawar da zai yi da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ya ce, Buhari zai ƙaddamar da cibiyar ta NASENI a wata rana ta daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *