CMG ya shirya tarukan yaɗa ruhin taron wakilan JKS karo na 20 a ƙasashen Afirka

Daga CMG HAUSA

Cibiyar dake tsara shirye-shirye da harsunan ƙasashen Asiya da Afirka ta babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG da karamin ofishin jakadancin ƙasar Sin dake yankin Zanzibar da hukumar watsa labarai na yankin, sun shirya taron yada ruhin babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 mai taken “Sabon tafarki da makoma ta bai daya” a yankin Zanzibar na ƙasar Tanzaniya a ranar 26 ga wannan wata, agogon ƙasar.

Yaron da ya samu halartar babban ƙaramin jakadan ƙasar Sin dake yankin Zhang Zhisheng, da babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai da matasa da al’adu da wasannin motsa jiki ta gwamnatin juyin juya hali ta Zanzibar Fatima Hamad Rajab, da shugaban hukumar watsa labarai ta yankin Hassan, da shugabanni da manema labarai na manyan kafofin watsa labarai sama da 20 dake yankin.

Yayin taron, wakilan ƙasar Sin sun yi bayani kan babban sakamako da babbar ma’anar babban taron wakilan JKS karo na 20, da fasahohin da JKS ta samu wajen gudanar da harkokin ƙasa, duk wadannan sun samu yabo da amincewa daga mahalartan taron.

Babban ƙaramin jakadan ƙasar Sin dake yankin Zanzibar Zhang Zhisheng shi ma ya gabatar da jawabi yayin taron, inda ya bayyana cewa, ƙasar Sin wadda ta shiga sabon tafarki na zamanintar da ƙasa mai bin salon tsarin gurguzu tana son ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakaninta da Tanzaniya, domin gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka ta bai ɗaya.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kula da watsa labarai da matasa da al’adu da wasannin motsa jiki ta gwamnatin juyin juya hali ta Zanzibar Fatima Hamad Rajab ita ma ta yaba wa babban sakamakon da al’ummun Sinawa suka samu ƙarƙashin jagorancin JKS.

Inda ta bayyana cewa, taron da aka shirya zai taimaka wa kafofin watsa labarai na yankin Zanzibar wajen ƙara fahimtar manufofin tafiyar da harkokin ƙasa na JKS, haka kuma zai taimakawa kafofin watsa labarai na Zanzibar yayin da suke gabatar da labaran dake shafar ƙasar Sin, da ingiza haɗin gwiwa da cudanya a fannoni daban daban tsakanin sassan biyu wato ƙasar Sin da Zanzibar.

Sannan a kwanakin nan ne, hukumar CMG Africa ta gudanar da wasu bukukuwa na musamman kan “Sabon tafarki na ƙasar Sin da Duniya” a ƙasashen Kenya da Afirka ta kudu bi da bi.

A yayin taron tattaunawa ta musannan da ya gudana a ƙasar Kenya kan “Sabon tafarki na ƙasar Sin da duniya”, jakadan ƙasar Sin dake Kenya Zhou Pingjian, ya tattauna da editoci da ‘yan jaridu sama da 40 daga ƙasashen Afirka.

Jakada Zhou Pingjian ya bayyana cewa, ƙasar Sin tana son ƙara samar da gudummawar albarkatu ga hadin gwiwar ƙasa da ƙasa, da kokarin rage gibin dake tsakanin Arewaci da Kudanci, da samar da goyon baya da taimako ga ƙasashe masu tasowa wajen ingiza samun bunƙasuwa.

Bugu da kari, an shirya taron ƙara wa juna sani kan “Sabon tafarki na ƙasar Sin da duniya” a ƙasar Afirka ta kudu wanda CMG tare da haɗin gwiwar jami’ar Johannesburg ta ƙasar Afirka ta Kudu suka ɗauki nauyin shiryawa tare cikin nasara a birnin Johannesburg.

Inda aka gayyaci wakilai da dama daga majalisar dokokin Afirka ta Kudu da ɓangaren gwamnati, da jami’an ilimi domin halartar taron.

Masu Fassarawa: Ibrahim Yaya da Jamila Zhou