Ba ni na kashe Ummita ba, inji ɗan Chana a gaban kotu

Daga AMINA YUSUF ALI

Mutumin nan ɗan asalin ƙasar Chana mai suna Geng Quangrong ya musanta zargin kashe budurwarsa mai suna Ummita da ake yi masa a gaban Babbar Kotun Kano. 

An gurfanar da Geng Quarong a gaban wata kotu wacce take zamanta a kan titin Miller Road dake jihar Kano. Inda Geng wanda aka kama dumu-dumu yana yi wa budurwarsa Ummukulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita, yankan rago ya ƙeƙasa ƙasa ya ƙi amsar laifinsa. 

A ranar 27 ga watan Oktoba, 2022 ne yayin zaman kotu ne dai Alƙalin kotun mai suna, Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya ba da umarnin a karanta wa wanda ake zargin laifin da ya aikata da yarensa na canisanci. A nan ya musanta zargin da ake masa na kashe masoyiyar tasa mai shekaru 23 a Duniya.  

Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata ne aka dakatar da shari’ar a kan buƙatar Geng Quarong na a ba shi lauya ko tafinta wanda yake jin harshensa na Canisanci.  

To bayan an dawo da  zaman kotun ne dai hukumar lauyoyi ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Antoni Janar na Kano, Musa Abdullahi Lawal, suka samar da tafinta, tare da taimakon ofishin jakadancin Nijeriya, Mista Guo Cumru shi ne tafintan. 

Kotun ta nemi Mista Cumru a kan ya bayyana gaban kotun ya dinga fassaro wa mai laifin tuhumar da ake masa daga Turanci zuwa Canisanci. 

Shi kuma lauyan mai tuhuma ya karanto wa Geng laifinsa wanda ya sava wa da dokar sashe na 123 da ƙaramin sashe na 1a a dokar laifi ta kotun laifuffuka ta Kano. Sai dai mai laifin ya musanta laifin da ake tuhumarsa. 

Akan haka Antoni Janar na Jihar Kano ya roƙi kotun da ta ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 14, 15, da kuma 16 ga watan Nuwamba, 2022, domin a samu sararin tattarawa da gabatar da shaidu a gabanta.

Shi dai wannan Bacanishe mai suna Mista Geng ana zargin ya yi sanadiyyar mutuwar budurwarsa Ummita ne bayan yin kutse zuwa ɗakinta da hallaka ta hanyar yi mata yankan rago.