Sojoji sun fatattaki mayaƙan ISWAP a Neja

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Jihar Neja sun ce, sojoji sun fatattaki wasu ‘yan ta’addar da ake zargin mayaƙan ISWAP ne a Jihar bayan yinƙurin da suka yi na neman kuɓutar da ‘yan uwansu ya gamu da tasgaro.

Bayanai daga jihar sun ce, ‘yan ta’addar sun yi ƙoƙarin kutsawa inda ake tsare da wasu jagororinsu a yankin New Bussa don ƙwato su inda suka gamu da ajalinsu.

Majiyarmu ta ce, da ma dai sojoji sun tsammaci zuwan ‘yan ta’addar, wanda hakan ya sa suka yi musu kwanton-ɓauna.

Majiyar ta ƙara da cewa, duk da dai lamarin ya faru ne cikin dare, hakan bai hana ‘yan ta’addar faɗawa tarkon sojojin ba.

An ce aƙalla gawargwakin ‘yan bindigar guda bakwai aka gano da safe yayin da aka kama ɗaya daga cikin kwamandojin da suka jagoranci kai harin.