Sake fasalin Naira zai sa masu garkuwa fara neman biyan fansa da Dala – Sheikh Gumi

Daga BASHIR ISAH

Fitaccen malamin Islaman nan Ahmad Gumi, ya ce batun sake tsarin Naira zai sa ‘yan fashin daji su fara neman a biya kuɗin fansa da Dalar Amurka kafin su sako waɗanda ke hannunsu.

Haka nan ya ce, matakin tamkar karya tattalin arzikin ƙasa ne ga ‘yan Nijeriya, musamman mazauna karkara.

Don haka malamin ya ce ba ya tare da Babban Bankin Nijeriya (CBN) a kan wannan ƙudiri da ya sa gaba.

Ya ƙara da cewa, kashi 80 na ‘yan Nijeriya, musamman mautanen karkara, sun fi gane ma hada-hada da kuɗi a hannu.

Cikin bayanin da ya fitar, malamin ya ce ba yanzu ne lokacin da ya dace CBN ya ɗaga wannan batu ba.

Yana mai cewa, duk wani mataki da za a ɗauka wanda zai ƙara kassara kuɗin ƙasa ba alheri ba ne ga ƙasa da al’ummarta.

A cewarsa, wannan mataki ba zai taɓa masu garkuwa da mutane ba, domin kuwa tuni za su shiga neman fansa ta amfani da Dala da sauran kuɗaɗen duniya wanda zai ƙara jefa rayuwar jama’a cikin mawuyacin hali.