Yadda zanga-zangar direbobin BUA ta ƙare da sallamar ma’aikata 700

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin BUA, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin hada-hadar siminti da sarrafa abinci a Nijeriya, ya sallami kimanin direbobin manyan motoci 700 a cibiyarsa ta Obu-Okpella da ke Jihar Edo, bayan wata zanga-zangar lumana da ma’aikatan suka gudanar a watan Disambar 2025.

Direbobin sun ce sun fito ne domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda aka ware su daga cikin rabon kyautar jinƙai ta Naira Biliyan 30 da Shugaban kamfanin, Abdul-Samad Rabiu, ya sanar domin tallafa wa ma’aikatan da suka daɗe suna aiki a rukunin kamfanin.

A cewar wasu daga cikin direbobin da abin ya shafa, kuzin da darajarsa ta kai kusan dala miliyan 20.7 an raba su ne tsakanin manyan jami’ai da sauran rukunan ma’aikata, amma ɓangaren sufuri, wanda suka bayyana a matsayin ginshiƙin ayyukan kamfanin, bai samu komai ba.

Wani direba mai suna Silas Simon ya shaida cewa bayan sun gano ba su ci gajiyar shirin ba, sun gabatar da koke-koke a cikin gida amma ba a bi su da wata mafita ba.

Daga bisani ne suka shirya zanga-zangar lumana a ranar 24 ga Disamba, 2025. Sai dai a maimakon a warware matsalarsu, sun ce kamfanin ya ba su takardun sallama.

A cewarsa, yawancinsu ba su samu ko sisi na haƙƙoƙin sallama ba, lamarin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Ya ƙara da cewa, wasu direbobin sun shafe sama da shekaru 10 suna aiki a kamfanin ba tare da sun taɓa cin gajiyar wasu tsare-tsaren jinƙai da ake bai wa ma’aikatan da suka daɗe ba.

Wani direba, John Obi, wanda ya ce ya fara aiki da kamfanin tun 2015, ya tabbatar da cewa an ba da takardun sallama ne ranar 27 ga Disamba, kwanaki uku bayan zanga-zangar.

Ya ce, an gayyace su sashen gudanarwa da sunan taro, amma aka miƙa musu takardun sallama.

Direbobin sun kuma zargi kamfanin da kin ba su wasu muhimman haƙƙoƙi kamar alawus ɗin gida da inshorar lafiya, duk da hatsarin da aikinsu ke tattare da shi.

A cewarsu, albashinsu na kai tsakanin N65,000 zuwa N120,000 a wata, kuma ba sa cikin tsarin kula da lafiya na kamfanin.

Sun bayyana cewa idan wani direba ya rasu ko ya kamu da rashin lafiya, su kan haɗa kuɗi a tsakaninsu domin magance matsalar.

Wani direba mai suna Friday James ya ce taƙaddama tsakanin sashen sufuri da mahukunta ta dade tana faruwa, musamman kan batun alawus ɗin gida da kuma tantance ko su ma’aikatan kai tsaye ne ko na kwangila.

Direbobin sun ce rabon kyautar biliyan N30 ne ya sake tayar da ƙura, bayan sun gano an riga an raba kuɗin ba tare da sun samu komai ba. Hakan ne ya sa suka yanke shawarar gudanar da zanga-zangar lumana.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kamfanin BUA bai fitar da wata sanarwa ba dangane da zargin da ake yi masa.

By ukarofi