Yahaya Bello zai yi bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara a gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotu ta tura tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello zuwa Gidan Yarin Kuje kan almundahanar Naira biliyan 110.4.

A ranar Talata Mai Sharia Maryann Anenih ta bayar da umarnin tare da dage sauraron shari’ar zuwa ranar 29 da watan Janairun 2025.

Umarnin na zuwa ne bayan Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arzikin ƙasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan wanda suka jima suna wasan ɓuya da shi.

Tun da farko alƙalin ta yi watsi da neman belin Yahaya Bello, wanda ta ce an yi riga malam masallaci, saboda an shigar da buƙatar ce kafin a kama shi ko a gurfanar das hi a kotu, don haka ba ta da amfani.

Ta ci gaba da cewa, “Shi ma buƙatar belin da aka shigar nan take ya yi riga malam masallaci, don haka ba a amince da shi ba.”

Yahaya Bello da wasu mutum biyu dai suna fuskantar shari’a ne kan zargin karkatar da Naira biliyan 110.4 a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kogi.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da su tana tuhumarsu da laifuka 16 tare da jami’an gwamnatin nasa, Abdulsalami Hudu da kuma Umar Oricha wadanda ake zargi da haɗa baki da kuma mallakar gidaje a unguwannin masu kuɗi a Abuja da birnin Dubai na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuɗinsu ya kai biliyan N110.4.

Sai dai alƙalin ta bayar da belin hudu.