Yajin aiki: Kaso 90 na buƙatunmu ba na kuɗi ba ne, inji ungozomomi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugabar Ƙungiyar Ungozomomi ta Ƙasa (NANNM) reshen Jihar Kuros-Riba, Josephine Bassey ta bayyana hakan yayin magana game da yajin aikin gargaɗi na mako guda da ƙungiyar ta shiga, wanda aka fara a ranar 30 ga watan Yuli.

Ta faɗi haka ne yayin ganawa da manema labarai, ranar Alhamis inda ta ce mafi yawancin buƙatun nasu sun ta’allaƙa ne da matsalolin gudanarwa da aiwatar da su, waɗanda suka shafi takardun tsare-tsare da tabbatar da hukunce-hukuncen kotu.

Ta kuma ce, akwai matsalar da ta shafi amincewa da wasu buƙatu na tsawon lokaci daga kwamitin ƙasa akan harkokinsu, waɗanda suka haɗa da shirin ungozomomi na nursing scheme of service da samar da ɓangaren ungozomanci a Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasa.

Ta ƙara da cewa, akwai buƙatar gyara akan dokokin bada alawus ga ungozomomi da naɗa su cikin ofisoshin cibiyoyin lafiya.

Haka kuma, akwai buƙatar a ɗauki wasu ƙarin ungozomomi aiki a asibitocin faɗin Nijeriya saboda ƙarancin su, kamar yadda ta bayyana.

By Babaji