Benuwai: ‘Yan sanda sun ceto ɗaliban makarantar lauyoyi shida da aka yi garkuwa da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Jihar Benuwai sun ce jami’an ƴan sanda sun yi nasarar ceto ɗaliban Makarantar Lauyoyi na reshen Yola guda shida da aka yi garkuwa da su a ranar 26 ga Yuli, 2025 a lokacin da suke hanyar komawa Jihar Adamawa daga Anambara.

A daren ranar Asabar wayewar Lahadi ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin iyakar Wukari a Jihar Taraba da Jihar Benuwai.

Kakakin rundunar ƴan sandan, Edet Udeme a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, ta ce an ceto ɗaliban cikin aminci.

Haka kuma, an miƙa su ga iyalansu a safiyar Juma’a, 1 ga watan Agusta, 2025.

Ta ƙara da cewa, jami’ansu na cigaba da aiki tuƙuru wajen bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma tsaro a faɗin sassan ƙasar.

By Babaji