
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Ilimi, Ali Pate, ya ce Ƙungiyar Ungozomomi ta Ƙasa (NANNM) ta janye yajin aikin gargaɗi da ta shiga kwanaki biyu da suka gabata a faɗin Nijeriya.
Pate ya bayyana haka ne ga manena labarai jim-kaɗan bayan kammala wani zaman sirri da ya ƙunshi jagororin ƙungiyar a Abuja inda aka cimma yarjejeniya akan wasu al’amura da suka shafi batun.
A ranar 29 ga watan Yuli NANNM ta tsunduma yajin aikin bayan abinda ta kira da gazawar gwamnati na amsa gargaɗin da ta bayar wanda ya ƙare a ranar 14 ga watan.
Ƙungiyar ta fara yajin aikin ne sakamakon kokawa na tsawon lokaci game da walwalar mambobinta da suka haɗa da rashin kyan wuraren gudanar da ayyukansu da kuma nuna halin ko-in-kula da gwamnati ta yi akan magance matsalolin.
Haka kuma, ƙungiyar ta nemi a inganta harkokin biyan mambobin nata alawus a baki ɗaya cibiyoyin lafiya da ke sassan ƙasar.
