’Yan Arewa mazauna Kudu maso Yammacin Nijeriya sun yi taron haɗin kai a Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Kungiyar ‘Yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya ta gudanar da wani babban taron haɗin kai a birnin Legas, domin ƙarfafa zumunci da haɗa kan al’umma wajen tafiyar siyasar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, gabanin zaɓen shekarar 2027.

An gudanar da taron ne ranar Alhamis da ta gabata a harabar babban ɗakin taro da ke Ikeja, inda daraktan janar na tafiyar Tinubu a jihohin Kudu maso Yammacin Nijeriya, Alhaji Shehu Usman Jibirin Sampam, ya jagoranci taron a matsayin sabon jagoran tafiyar a yankin.

Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa maza da mata daga jam’iyyar APC, da suka haɗo da su daga jihohin Legas, Ogun, Oyo, Osun, Ondo da Ekiti. Haka kuma an samu halartar sarakunan gargajiya na Hausawa mazauna Legas da kewayenta, tare da ‘yan kasuwa da manyan jagororin al’ummar Arewa mazauna Kudu maso Yamma.

Daga cikin fitattun baƙin da suka halarci taron akwai Alhaji Abdullahi Umar Dan Asabe, Marafan Legas, da Alhaji Basi, Sarkin Hausawan Isheri kuma shugaban kasuwar shanu, da Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma, Shugaban ƙungiyar Arewa Community ta Jihar Legas. Haka kuma Alhaji Muhammadu Dan Damma Yabo, uban Kungiyar Arewa Community a Legas kuma shugaban kasuwar Doya ta Mile 12 ya halarci taron, tare da wasu ‘yan majalisar dokokin Jihar Legas da shugabannin kasuwar Mile 12.

A yayin taron, manyan ‘yan siyasar APC da suka halarta sun gabatar da jawaban su daban-daban, inda suka bayyana farin cikinsu matuƙa game da haɗin kai da aka samu tsakanin al’ummar Arewa mazauna Kudu maso Yamma da tafiyar Tinubu. Sun kuma yabawa Daraktan Janar, Alhaji Shehu Usman Jibirin Sampam, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen kawo cigaba da daɗaita al’umma cikin tafiyar.

Da yake nasa jawabin, Alhaji Shehu Usman Jibirin Sampam ya fara da godiya ga Allah bisa ikon da ya ba shi na ganin an gudanar da taron karo na farko cikin nasara.

Ya bayyana jin daɗin sa game da yadda jama’a suka amsa kiran taron, yana mai fatan alheri ga duk mahalarta. Ya kuma bayyana fatan nan gaba idan aka sake shirya taron karo na biyu, adadin mahalarta zai ƙaru fiye da yadda aka gani a wannan karo.

By ukarofi