‘Daga Umar Garba a Katsina
‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a garin Mai Dabino dake ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina inda suka kashe mutane tara(9) suka ƙone gidaje huɗu (4) da motocin ‘yan kasuwa tara (9) tare da yin garkuwa da mata da ƙananan yara fiye da hamsin a yayin harin da suka kai a garin na Mai Dabino.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Blueprint Manhaja cewa ‘yan ta’addar sun kutsa kai da misalin ƙarfe goma na dare, inda suka shafe kimanin sa’o’i bakwai suna ta’addanci a garin sun kashe mutane tare da ƙone ƙananan yara.Kazalikai, sun yi garkuwa da mata da ƙananan yara fiye da hamsin inda suka shiga daji da su, tare da ƙona motocin ‘yan kasuwa dake kan hanyar a yayin harin.
‘Yan bindigar ba su tsaya nan ba, don kuwa sun riƙa bi gidaje da shaguna suna sace kayan abinci, inda daga bisani suka ƙone ragowar kayan abincin da suka kasa ɗauka inji majiyar Manhaja.
Yanzu haka dai duk mazauna garin sun tsere don gudun dawowar ‘yan bindigar.Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar ta Ɗan Musa a majalisar dokokin jihar Katsina Aminu Sai Baba, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da yin Alla-wadai da harin, ya kuma yi kira ga gwamnati ta kawo wa mazauna garin ɗaukin gaggawa.Da yake tabbatar da kai harin, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce, mutane bakwai ne aka kashe kuma a halin yanzu an tura jami’an tsaro yankin don dawo da zaman lafiya.”
A jiya, 23 ga watan Yuni, 2024, wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai, sun yi ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi, inda suka kai hari ƙauyen Maidabino, a ƙaramar hukumar Ɗanmusa sun harbe mutane kusan bakwai (7).A halin yanzu ana ci gaba da bincike, rundunar za ta sanar da halin da ake ciki game da lamarin a kan lokaci,” in ji shi.
