Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai a kan bubura sun kai hare hare a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Kankiya ta jihar Katsina.
Sai dai jami’an tsaro ƙarƙashin DPO na Kankia sun kai wa al’ummar wuraren ɗauki bayan da suka sami bayanan sirri na yadda ‘yan bindigan suka mamaye ƙauyukan.
Bayan ɗauki ba daɗi na tsawon lokaci da jami’an tsaron, yan bindigan suka gudu suna ɗauke da raunuka da dama.
Kwamishinan cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Danmusa wanda ya sanar da cewa ya ce jami’an tsaron sun sami nasarar kama babura da dama wanda yanzu haka suna ofishin yan sanda a Kankiya.
Sai a cewar kwamishinan bayan wani lokaci duk a ranar da suka kai farmaki na farko, ƙasurgumin dan bindiga Mohammadu Fulani da mutanen da suka sake kai hari a ƙauyukan Gyara, Kunduru da Gwalgoro na karamar hukumar Kankiya inda suka kashe mutane 11.
Dr Danmusa ya ce gwamnatin katsina tayi Allah wadai da wannan hare haren na rashin imani da yan bindiga su kai wa al’ummar ƙauyukan waɗanda basu ji basu gani ba.
Haka gwamnatin jihar Katsina ta miƙa ta’aziya ga iyalan waɗanda aka kashe tare da tabbatar masu da cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa na bakin ƙoƙarin ta na ganin an kawo ƙarshen wannan ta’addanci a faɗin jihar.
Haka kuma gwamnatin jihar ta jinjinawa jami’an tsaro bisa nuna kwarewa da jajircewa wajan yaƙar waɗannan ‘yan bindiga.
