Daga USMAN KAROFI
Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wani masallaci a garin Bushe da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka sace liman da wasu masallata da suka fito sallar asuba a safiyar Alhamis. Maharan sun afkawa masallacin ne da sanyin safiya, inda suka tafi da mutane fiye da goma.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara aiki tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro don ceto waɗanda aka sace. Ya ce rundunar ‘yan sanda tana ƙoƙarin ganin an kuɓutar da su cikin gaggawa.
A nasa ɓangaren, ɗan majalisar jihar Sakkwato mai wakiltar yankin, Sa’idu Ibrahim, ya bayyana cewa aƙalla mutum goma ne aka sace yayin harin. Ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro suka ɗauki matakin gaggawa domin ganin an kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.