‘Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Kogi sun buƙaci fansar milyan N30

Daga WAKILINMU

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da Sarki Adogu na Eganyi, Alhaji Mohammed Adembe a yankin ƙaramar hukumar Ajaokuta da ke jihar Kogi.

Bayanai sun nuna an sace basaraken ne da yammacin Talatar da ta gabata a kan hanyar Okene-Eganyi.

Wannan al’amari na zuwa ne sa’o’i 72 da sako Sarkin Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Hassan Adamu, bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da iyalansa.

Kazalika, sace basaraken Kogin na zuwa ne kwanaki uku da sace babban manaja a kamfanin haɗa magunguna na AZECO Pharmaceutical, AbdulAzeez Obajimoh, a Ozuwaya da ke Okene.

Wata majiya ta kusa da sarkin ta bayyana wa manema labarai cewa kafin aukuwar lamarin, sarkin ya bar garin Okene shi kaɗai a mota da misalin ƙarfe 4 na yamma ran Talata da nufin zuwa ƙauyen Eganyi inda aka sace shi a tsakanin Ebiya da Eganyi.

Majiyar ta ci gaba da cewa daga bisani, masu garkuwar sun yi magana da ahalin sarkin da misalin ƙarfe 1 na rana a ran Laraba inda suka buƙaci a biya su fansar milyan N30 kafin su sake shi.

Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, Mr William Ayah, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da cewa sun tura dakaru na musamman don su binciko maɓuyar ɓatagarin sannan su kuɓutar da sarkin.