Yau Buhari zai ziyarci Kano

A yau Alhamis Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Kano inda ake sa ran ya ƙaddamar da ginin sabon layin dogo daga Kano zuwa Kaduna.

Layin dogon da Buhari zai ƙaddamar a Kano shi ne zai haɗe da na Kaduna zuwa Abuja zuwa Legas.

Wannan na daga cikin ayyukan da gwamnatin Buhari ta ƙuduri aniyyar yi domin bunƙasa fannin tattalin arzikin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *