Gangamin siyasa: Majalisar Zamfara ta gayyaci Mataimakin Gwamna kan zargin take doka

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta gayyaci Mataimakin Gwamnan Jihar, Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, tare da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hussaini Rabiu, da su bayyana a gabanta ya zuwa ranar Talata, 27 ga Yulin 2021.

Majalisar ta cim ma matsayar aika gayyatar ne s zamanta na jiya Larabar.

Dalilin gayyatar majalisar ya biyo bayan wani ikirarin gudanar da gangamin siyasa da Mataimakin Gwamnan ya yi a ranar Asabar din da ta gabata, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kan al’ummomin ƙaramar hukumar Maradun a daidai lokacin da jihar ke jimami saboda addabar da ‘yan bindiga suka yi mata.

Ƙudirin da Hon. Yusuf Alhassan Kanoma (mai wakiltar Maru ta Arewa) ya gabatar wa majalisar kan lamurra masu muhimmanci ga majalisar, shi ne ya yi silar ɗaukar matakin gayyatar Muhammad.

Hon. Kanoma ya yi Allah wadai da ayyuka da kuma kalaman Barista Mahdi Aliyu a yayin taron siyasar da suka gudanar ran Asabar da ta gabata wanda Mataimakin Gwamnan ya shirya ƙasa da awanni 24 da kai munanan hare-haren ramuwar gayya da ’yan bindiga suka kai wa al’ummomin Faru a ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar.

Kanoma ya kara da cewa, yayin da jihar ke cikin baƙin ciki da alhini game da kisan mutane sama da 56 da ba su ji ba ba su gani ba, Mataimakin Gwamnan bai nuna wata nadama ba game da kashe-kashen amma ya shagaltu da shirya taron siyasa duk da rashin dacewar hakan da Kwamishanan ‘Yan Sandan jihar ya nuna masa.

Ya bayyana matakin da Mataimakin Gwamnan ya ɗauka a matsayin rashin bin tsarin dimokuraɗiyya.

Bayan zazzafar muhawara a kan lamarin, Kakakin Majalisar, Rt Hon. Nasiru Mu’azu Magarya, ya ce Majalisar ta zartar da ƙudurin gayyatar Mataimakin Gwamnan da Kwamishinan ’Yan sanda na Jiha. Ya ƙara da cewa za su bayyana a gaban Majalisar a ranar Talata 27 ga watan Yulin 2021.

Manhaja ta ruwaito cewa tun lokacin da Gwamnan Jihar, Bello Mohammed Matawalle, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, mataimakinsa Mahadi Aliyu Gusau ya ƙi bin shi, yana mai cewa yana nan daram a PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *