Gobe RATTAWU za ta gudanar da babban taronta a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Kawo yanzu an kammala shirye-shirye tsaf don gudanar da taron wakilai na ƙasa na Ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin da ‘Yan Wasan Dandamali ta Nijeriya (RATTAWU) a Gusau Babban birnin jihar Zamfara da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a 16 ga Yuli, 2021.

Da yake magana da manema labarai a Gusau a Yammacin yau Laraba, Shugaban RATTAWU na ƙasa, Kwamared Kabir Garba Tsanni, ya ce tuni wakilan jihohi 36 na shugabannin ƙungiyar sun fara sauka a Gusau don halartar taron ƙungiyar da za a yi gobe Juma’a.

Tsanni ya bayyana ƙwarin gwiwa kan shirin da kwamitin tsare-tsaren taron ya yi don tabbatar da komai ya gudana cikin nasara.

Haka nan, ya wa Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle game da karɓar baƙuncin taron a Jihar ta Zamfara.

A ƙarshe, Tsanni ya ba da tabbacin taron zai gudana cikin lumana da kwanciyar hankali, tare da yin kira ga mambobin RATTAWU da su zama jakadu nagari a dun inda suka tsinci kansu.