Daga UMAR GARBA a Katsina
Alƙalin kotun shari’ar musulunci, Mohammad Mukhtar ya tsallake rijiya da baya bayan wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka yi yunƙurin sace shi ko kuma kashe shi gaba ɗaya.
‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai hari a garin Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu inda suka yi dirar mikiya a wata kotun Shari’ar Musulunci da rana tsaka a jiya Laraba, a dai dai lokacin da alƙalin da sauran ma’aikatan kotu ke gudanar da aikinsu.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kutsa cikin harabar kotun a yunƙurin da suka yi na garkuwa ko kuma kashe alƙalin kotun, Mohammed Mukhtar.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ɓarayin sun kutsa kai cikin harabar kotun inda suka riƙa yin harbi kan wai uwa da wabi, tare da tambayar ina alƙalin ya ɓoye.
Sai dai alƙalin ya lura da ɓarayin tun kafin su ƙaraso, lamarin da ya bashi damar tsallake wa ta tagar kotun a yayin da sauran ma’aikata suka bi bayansa, kamar yadda shaidun gani da ido su ka bayyana wa majiyar Blueprint Manhaja.
“Ɓarayin dajin sun shigo cikin ɗakin shari’a suna ta harbe harbe, suna tambayar ina alƙalin ya ke, sai dai an yi sa’a ya fice ta taga tun kafin su ƙaraso, wani ɗan achaɓa ne ya ɗauke shi suka gudu kafin su iso.” Kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida.
Daga bisani maharan sun bayar da saƙo a faɗa wa alƙalin, a cewar su idan suka sake dawo suka same shi a cikin kotun yana aikín zartar da hukunci za su kashe shi.
Wannan hari ya jefa tsoro da razani a zukatan mazauna garin na Gwarjo da ke ƙaramar hukumar Matazu, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi a Katsina da ke fama da matsalar ‘yan bindiga.
