‘Yan bindinga sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen jihar Katsina, Alhaji Amadu Surajo a ƙauyen Mai Rana da ke ƙaramar hukumar Kusada ta Jihar Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin da yammacin ranar Lahadi, cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a birnin Katsina.

“DPO ya sanar da ni cewa lamarin ya faru ne a daren jiya,” in ji kakakin rundunar.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu ya bayyana yadda lamarin ya faru.

Eh, jiya ne ‘yan bindiga suka kashe shi,” in ji Mu’azu.

‘Yan ta’addar sun kuma kashe wasu mutane uku tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar da ta gabata zuwa wayewar garin Lahadi lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari ƙauyen.

Blueprint Manhaja ta kuma samu labarin cewa ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da matan marigayin guda biyu, tare ‘ya’yansa mata, ɗaya daga ciki na karatun digiri na farko a ɗaya daga cikin jami’o’in ƙasar nan.

Sai dai wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta ce daga baya ‘yan bindigar sun sako uwar gidan marigayin.

An yi janazar marigayi shugaban ƙungiyar ta Miyetti Allah tare da sauran mutane uku da ‘yan bindingar suka hallaka.

By ukarofi