Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya amince da buƙatar ajiye aikin Kwamishinan bibiyar ayyuka Hon Engr Muhammad Diggol ba tare da ɓata lokaci ba.
Wannan na ɗauke ne a wata sanarwa da Kakakin gwamnan Sanusi Bature ya fitar ga manema labarai a daren jiya.
Diggol wanda akayi ma naɗin matsayin kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano bayan samun nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen da ya gabata na 2023, daga bisani gwamnan ya canza mashi ma’aikata ta bibiyar ayyukan gwamnati da tabbatarwa.
Gwamna wanda ya miƙa saƙon godiyar shi ga tsohon Kwamishinan bisa dukkan ƙoƙarin da ya yi wajen gudanar da aikin shi da zamo misali a lokacin da yake riƙe da kujerar kwamishina kuma ɗaya daga cikin mambobi na majalisar zartarwa.
Gwamna Abba ya kuma yima Injiniya Muhammad Diggol dukkan fatan alkhairi a rayuwar sa baki ɗaya.
