Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban Asibitin Best Choice dake jihar Kano, Alhaji Auwal Lawal Muhammad ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 da haihuwa inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da himma wajen yi wa al’umma hidima.
Cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannunsa, Shugaban asibitin yaba da nasarorin da gwamnan ya samu a fannin Ilimi, Kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, yana mai cewa hakan na nuni da irin kishi da jajircewarsa wajen cigaban jihar.
Ya kuma yaba wa ƙoƙarin da gwamnan ya yi cikin ƙanƙanin lokaci inda ya ce hakan abin koyi ne ga sauran gwamnoni, sannan ya bar tarihi da za a jima ana tunawa da shi.
Ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda Kano ke sauyawa cikin gaggawa ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Salon shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf a cewar Lawal ya kawo sauyi mai kyau ga jihar Kano.
“Yunƙurinsa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana da shugabanci na gari ya sa jama’a ke girmama shi da kuma yaba masa kan ayyukan da ya ke aiwatarwa.”
Har’ilayau Ya jinjina da ayyukan da gwamnan ya yi a fannin ilimi da suka haɗa da gina sabbin makarantu, gyara waɗanda ake da su, da kuma samar da kayayyakin ilimi.
Kwamared Auwal Lawan ya ƙara da yaba masa bisa sadaukarwa da tsantsar tausayi da yake nunawa, wadanda hakan ke tasiri a rayukan al’umma.
A lokacin da Gwamna Abba ke murnar cika shekaru 62 a duniya, Lawal ya yi addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya da basira da kuma ƙwarin-gwiwa na cigaba da yi wa al’ummar jihar hidima.
