Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bai wa ƙungiyar masu yaɗa manufar gwamnatin shi Kwankwasiyya/Abba Gida-Gida Media Forum tallafin naira miliyan 30.
Gwamna wanda ya tabbatar da haka yayin da yake buɗe taron bada tallafin naira 200,000 da shugabanin wannan Ƙungiya suka bai wa ya’yan wannan Ƙungiya dan basu damar samo hanyar dogaro da kai gare su.
Gwamna Abba Kabir yace wannan yunƙuri da Ƙungiyar ta yi yana ɗaya daga cikin abinda wannan gwamnati ta sanya a matakin farko baya ga Ilimi dan kawar ma natasa dukkan tunanin da zai sanya su barin hanyar da ta dace.
”Mun sani da dukkan ayyukan ku kasancewar hakan yasa lokacin da aka aika mani da takardar gayyatar wannan taro lokacin ina waje sai na roƙi alfarmar a bari nadawo dan nima na tofa albarkacin bakina.
”Haka kuma ku da za’a baiwa wannan tallafi a yau bawai dan baku dashi bane sai dan ance kyautatawa akan abinda akeyi ne na ƙoƙarin ku.”
Sannan ya tabbatar da cewa za su cigaba da tallafawa wannan tafiya ta su don ƙara bada dukkan taimakon daya kamata dan ayyukan su ya ƙara samun karbuwa.
Gwamna ya kuma hori dukkan wanda ya samu wannan tallafi da yayi amfani dashi wajen inganta koda ɗan ƙaramin jari ne.
Shima a nashi jawabin Hon Alhajiji Nagoda yace kasancewar Gwamna Abba Kabir Dattijo ne wanda ya yi koyi da halin shugaban tafiyar Kwankwasiyya na duniya Rabiu Musa Kwankwaso a wajen gudanar da ayukan Alkhairi.
Nagoda yace wannan taro na da nasaba da tunawa da zagayowar haihuwar mai girma gwamna na cika shekaru 62 da haihuwa a duniya.
Haka kuma mai taimakawa gwamnan ya yi fatan samun cigaba da haɗin kan al’ummar jihar Kano da za’a samu damar ɗaukaka jihar.
