Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗe-naɗe muƙamai da dama da nufin ƙarfafa gwamnatinsa don gudanar da shugabanci nagari.
Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aiko wa Blueprint Manhaja a yammacin ranar Lahadi, ya bayyana waɗanda aka naɗa kamar haka:
Hon. Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mai bada shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai; sai Injiniya Ahmad a matsayin mai bada shawara na musamman kan ayyuka; da kuma Malam Sani Abdullahi Tofa a muƙamin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan ayyuka na musamman.
Kazalika akwai Hon. Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin shugaban Hukumar Kula da ƙananan Hukumomin Kano.
Da kuma Hajiya Ladidi Ibrahim Garko a matsayin shugabar hukumar ma’aikatan jihar Kano.
Waɗannan mutanen biyu da aka naɗa suna cikin tsoffin kwamishinonin da aka cire su kwanan nan.
Sanarwar ta cigaba da cewa Gwamna Abba ya shirya bikin rantsar da su a ranar Litinin 6 ga watan Janairun 2025 da misalin ƙarfe 11:00 na safe a zauren taro na Fadar gwamnatin Kano.
Za kuma a haɗa rantsuwar tasu da ta kwamishinoni bakwai da Majalisar Dokokin jihar ta tantance a kwanan nan, da kuma dukkan sabbin mashawarta na musamman da aka naɗa.
Sanarwa ta kuma ce naɗe-naɗen sun fara aiki ne a nan take.
