Gwamna Abba Kabir ya sake naɗa sabbin muƙamai

Spread the love

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir na Jihar Kano ya sake wasu sababin naɗe-naɗen muƙamai masu muhimmanci don cigaba da kawo canji mafi kyau a tafiya gwamnatin shi.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Malam Sanusi Ahmad Bature ya fitar ga manema labarai.

Sanusi Bature ya bada wannan sanarwar mai nuni da cewa waɗanda aka naɗa ɗin za su cigaba da aiki ba tare da ɓata lokaci ba, kama daga Hon Ahmad Muhammad Speaker a matsayin babban mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin yaɗa Labarai.

Sanarwar tace Ahmad ya bada gudunmuwar shi matuƙa bisa ƙwarewa wajen samun damar yin shugabancin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sau uku tare da riƙe tsohon sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC.

Haka sanarwar ta ce Malam Sani Abdullahi Tofa ya samu muƙamin mai bai wa gwamna shawara kan auyuka na musamman.

Malam Sani Tofa da wanda ake girmamawa kan ayyukan alherin shi, ya riƙe matsayi daban-daban da ya haɗa da Khadi a kotun shari’ar musulunci a Abuja da Jihar Kano,Kuma tsohon babban sakataren ma’aiktar kula da ma’aikata kuma tsohon darakta a a’aikatar shari’a.

Haka zalika gwamnan ya kuma kara naɗa tsohon Kwamishinan Kuɗi na jihar Hon Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin ciyaman ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da tsohuwar kwamishiniyar ma’aiktar tarihi da yawon buɗe ido Hajiya Ladidi Garko a matsayin ciyaman ma’aikatar kula da ma’aikata ta Jihar Kano.

Sanarwar tace wannan naɗe-naɗe da gwamnan yake yi zai ba masu riƙe da madafun ikon cigaba da zama a dunƙule wajen gudanar da ayyukan da za su ciyar da Jihar Kano gaba.

By ukarofi