‘Yan Boko Haram sun hallaka mutum bakwai a yankin Chibok

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mayaƙan Boko Haram sun halaka akalla mutum bakwai a wani hari da suka kai garin Koful da ke yankin ƙaramar Hukumar Chibok a jihar Borno, ta Arewa maso gabashin Nijeriya.

Mayaƙan sun dirar wa mutanen ne yayin da suke tsaka da zaman makokin wani mutumin da ya rasu, bayan yin jana’izarsa, inda suka bude wuta tare da bankawa wasu mujami’u da gidaje wuta.

Shugaban ƙaramar hukumar ta Chibok, Malam Modu Mustapha, wanda ya tabbatar wa da BBC afkuwar lamarin, ya ce mayaƙan sun kai harin ne da misalin ƙarfe biyar da yammacin Litinin.

”Jiya ne da misalin ƙarfe biyar da wani abu akwai rasuwa da aka yi ana wajen makokin rasuwa kawai a ankara kawai sai ga mashina, sai harbi kawai,” inji shugaban.

Ya ƙara bayani da cewa : ”Mutane sun tashi sun fara guduwa, ana binsu kamar dabbobi a jeji ana ta harbe su, ana ta ƙone-ƙone har Mangariba ta wuce mayaƙan Boko Haram suna nan sai da sojoji suka dawo sannan suka tafi.”

Mallam Modu ya ce an ɗan ɗauki lokaci kamar wata biyu mayaƙan na Boko Haram ba su kai musu harin ba sai a yanzu da suka kai musu wannan na ranar Litinin.

Ya ce mayaƙan sun yi wa garin dirar-mikiya ne a babura ɗauke da makamai, inda shigarsu ke da wuya suka nufi inda ake wannan zaman makoki suka buɗe wuta, mutane suna gudu suna binsu suna harbewa.

Bayan waɗanda suka rasu wasu kuma sun jikkata, ga kuma ƙone-ƙonen da suka yi na coci-coci da sauran gidajen jama’a.

Shugaban ya tabbatar wa da BBC cewa mayaƙan sun shiga garin ne daga ɓangaren Dambuwa.

Ya ce har zuwa lokacin da yake wannan bayani wasu mutanen da suka warwatsu a jeji ba su komo ba.

”Kafin wannan hari al’ummar wannan yanki waɗanda manoma ne da makiyaya suna gudanar da harkokinsu cikin walwala da komai,” ya ce.

Daman a baya-bayan nan hatta hukumomin jihar ta Borno sun tabbatar da cewa hare-haren mayaƙan Boko Haram da sauran ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi na ƙara dawowa bayan sun lafa na wani dogon lokaci da har an fara mayar da mutanen da suka yi gudun hijira a sakamakon rikicin.

Gwamnan jihar ta Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda jihar ke rasa wasu yankunanta sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram a baya-bayan nan.

Zulum ya bayyana haka ne yayin wani taro kan harkar tsaro da ya kira domin tattauna batun.

A makonnin baya-bayan nan ma, wasu da ake zargi ‘yan Boko Haram ne sun kashe sojojin Nijeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar – a hari da suka kai Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala.

Jihar ta Borno ta shafe tsawon shekaru tana fama da matsalar Boko Haram, wanda ya janyo asarar rayukan gomman mutane da kuma ta dukiya.

By ukarofi