‘Yan jarida 62 aka kashe a 2020 – UNESCO

Daga AISHA ASAS

Aƙalla ‘yan jarida 62 ne suka rasa rayukansu ta sanadiyyar aikin nasu. Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta tabbatar da hakan.

Hukumar ta ce a tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2020, sama da mutum 1,200 na ƙwararrun ‘yan jarida sun rasa rayukansu ta sanadiyyar neman labarai. Sai dai abin takaici kaso tara cikin goma na waɗanda wannan iftila’in ya faɗa wa ba a hukunta makasan su ba.

A shekara ta 2021, alƙaluma sun tabbatar da yawaitar kisan gillar da ake yi wa ‘yan jarida ba tare da haƙƙinsu ba, hakan yasa aka ware rana ta duniya don neman mafita ga wannan al’amari tare kuma da nuna muhimmancin ɗaukar mataki a kan mutanen da ke yi wa zaman lafiya barazana a tsakanin al’umma.

A cikin jawabinsa Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya António Guterres, ya ce, sanannen abu ne cewa, ma’aikatan yaɗa labarai na rasa rayukansu ta sanadiyyar kutsa wa wuraren da zaman lafiya ya ƙaranta don ɗaukar rahotanni. Sai dai abin mamaki shi ne yadda alkaluma suka tabbatar da yawan ‘yan jarida da ake kashewa a wuraren da ke zaune lafiya sun ninka waɗanda ake samu a wuraren da ake hatsaniya.

“A ƙasashe da dama, ƙaramin bincike kan cin-hanci, safarar mutane, take haƙƙin bil’adama ko matsalar muhalli kan iya sa rayuwar ɗan jarida a hatsari.” cewar babban sakataren.

Barazana ga rayukan ‘yan jarida hanya ce ta rufe bakinsu, wanda hakan ba ƙaramar illa ba ce ga al’umma, domin hana su damar sanin abin yake ɓoye, wanda zai sa su iya yanke hukunci ido rufe.

Aikin jarida na da matuƙar muhimmanci ga al’umma, don haka abin alhini ne halin da suke samun kansu a ciki na cin zarafi, azabtar wa da kuma kisan gilla duk don ƙoƙarin su na nema wa al’umma sani akan abin da ba su sani ba.

Kamar yadda Guterres ya faɗa, ” barazana ga rayukan manema labarai babban ci gaba ne ga al’amurran mutane.”

Ya kuma ƙara da cewa, ” idan ɗan jarida na fuskantar barazana, alamace ta ci-baya ga demokradiyya tare da tsari na dokoki.”

Rayuwar mata ‘yan jarida tafi zama cikin hatsari fiye da maza, kamar yadda wata takarda da Hukumar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar kan yaƙi da cin zarafin ‘yan jarida, inda ta ce, aƙalla kaso 73 bisa ɗari na ‘yan jarida mata da suka kuɓuta sun fuskanci zagi, baraza ta hanyar saƙwanin da ake turo masu ta yanar gizo.

Babban sakataren ya yi kira ga ƙasashe masu rijista da Majalisar Ɗinkin Duniya da su haɗa kai da ‘yan jarida tare da basu goyon baya, na ganin an zaƙulo waɗanda ke aikata wannan aika-aika, tare da yanke masu hukuncin da ya dace.

Babban Darektan UNESCO Audrey Azoulay ya ce, rashin hukunta masu kai hari ga ‘yan jarida alama ce ta rashin ‘yancin ɗan’Adam da kuma raunin dokokin ƙasa.” Ya kuma ƙara da kiran ranar ƙaddamar da wannan takarda a matsayin ‘ faɗin gaskiya yana da tsada.’

Daga ƙarshe ya yi kira ga shugabannin ƙasashen duniya da su kare lafiyar ‘yan jarida, kuma su tabbatar da hukunci mai tsanani ga waɗanda ke barazana ga aikinsu.

A shekarar da ta gabata, UNESCO ta bada horo ga aƙalla 23,000 daga cikin alƙalai da kuma lauyoyi kan ‘yancin faɗin abinda ya dace bisa kokokin ƙasashen duniya, da kuma bada kariya ga manema labarai, tare da yanke hukunci ga masu laifi.

Haka zalika, shirin ‘EndImpunity campaign’ na hukumar ya wayar da kan al’umma game da hatsarin da ke tattare da bayyanar da gaskiya da ‘yan jarida ke yi. “Ta hanyar samun damar faɗar gaskiya ne kawai za a samu zaman lafiya.” Inji Azoulay.