Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar ’yan jarida bakwai sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a Jihar Gombe.
Hatsarin ya rutsa da wata mota ƙirar bas ta ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), wacce ta ke ɗauke da ’yan jaridar, yayin da suke dawowa daga bikin auren wani abokin aikinsu da aka yi a ƙaramar Hukumar Kaltungo ta Jihar Jigawa.
Bayan kammala bikin cikin nasara, motar ta NUJ ta samu matsala a kan hanya a kusa da garin Kumo da ke ƙaramar Hukumar Akko, inda tayar motar ta fashe a lokacin da suke dawowa.
Lamarin ya sa direban ya rasa iko da motar, lamarin da ya haddasa ta fice daga hanya tare da shiga cikin daji.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Gombe, Samson Kaura, tare da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Harkokin Watsa Labarai na Fadar Gwamnatin Jihar, Ismaila Misilli, sun tabbatar da cewa mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a hatsarin, yayin da wasu huɗu suka jikkata.
An kai gawarwakin waɗanda suka rasu dakin ajiye gawa a Gombe, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti, inda ake ba su kulawar gaggawa.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai Zarah Umar, Manajan Labarai kuma Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna a Ofishin Uwargidan Gwamna; Manu Haruna Kwami, Manaja Harkokin Gudanarwa na NTA; Isa Lawan, Editan Fina-finai na NTA; da Musa Tabra, tsohon Manajan Labarai da ya yi ritaya.
Sauran sun haɗa da Aminu Adamu, babban direba; Adams Danladi na kamfanin StarTimes; da Judith Kutus, jami’ar yaɗa labarai a Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB).
Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu ta hannun Ismaila Misilli, inda ya bayyana alhininsa kan wannan mummunan ibtila’i, tare da yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan musiba ta girgiza jihar baki ɗaya, yana mai cewa jihar ta rasa abokan aiki nagari, masu hidimar jama’a da suka sadaukar da kansu wajen hidimar al’umma da kishin ƙasa. Ya ƙara da cewa, gwamnati na bibiyar halin da ake ciki tare da tabbatar da cewa duk wani tallafi da ake buƙata za a bayar.
A ƙarshe, gwamnan ya yi kira ga al’umma da su haza kai wajen addu’a, yana roƙon Allah Mazaukakin Sarki da Ya gafarta wa mamatan, Ya kuma kare jihar da kƙasa baki ɗaya daga sake aukuwar irin wannan mummunan lamari.
