Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen Wakilan Jaridu na Jihar Kano, ta gudanar da taron bayar da lambobin yabo na shekarar 2025 a ranar Lahadi, inda ta karrama tsofaffin shugabanninta, gaogaggun mambobi da kuma abokan ƙungiyar da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga aikin jarida da hidimar al’umma.
An gudanar da taron cikin dandali mai armashi a Tahir Guests Palace da ke Nasarawa GRA, Kano, inda ‘yan jarida, jami’an gwamnati, masana ilimi da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar suka halarta.
Rahotanni sun nuna cewa taron ya zama wata dama ta musamman ta sake haɗuwa da tsofaffin shugabannin ƙungiyar, waɗanda da yawa daga cikinsu yanzu suna aiki a jihohi daban-daban na ƙasar, tare da yin biki ga mambobin da suka kai manyan muƙamai a harkokin gwamnati da na sana’a.
A jawabin maraba, Shugaban Wakilan Jaridu na NUJ Kano, Alhaji Murtala Adewale, ya gode wa Allah Ta’ala bisa nasarar taron, yana mai bayyana daren a matsayin tarihi kuma mai ɗauke da ma’ana ta musamman.
Ya ce daren bayar da lambobin yabo na 2025 ya keɓanta saboda ya haɗa tsofaffin shugabanni goma na ƙungiyar a wuri guda, wasu daga cikinsu sun shafe sama da shekaru 30 suna aikin jarida.
A cewarsa, taron an shirya shi ne domin waiwaye kan tafiyar ƙungiyar, girmama kwazo da ƙwarewa, da kuma nuna godiya ga hidima ga bil’adama.
Ya ƙara da cewa, ana karrama mambobin da Allah ya ɗaukaka zuwa fannoni daban-daban na rayuwa, tare da abokan ƙungiyar da ke mara mata baya a kowane lokaci.
ɗaya daga cikin manyan baƙi, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Fagge, Barista M.B. Shehu, wanda aka karrama shi a matsayin Abokin ƙungiya, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba dokar gyaran haraji domin amfanin ‘yan ƙasa. Ya buƙaci shugabancin Majalisar Tarayya da su ɗauki batun da muhimmancin da ya dace, ganin tasirinsa ga al’umma da harkokin kasuwanci.
Shehu ya kuma shawarci ma’aikatan gwamnati, musamman ‘yan jarida, da su ci gaba da aiki tuƙuru wajen ƙarfafa haɗin kan Nijeriya, yana mai cewa haɗin kan ƙasa ya samo asali ne daga bambancin da ke cikinta, kuma Nijeriya ƙasa ɗaya ce da ba za a raba ta ba duk da bambance-bambancen siyasa, addini ko ƙabila.
A taron, an karrama fitattun mutane da dama a matsayin Abokan ƙungiya, ciki har da tsohon Shugaban NUJ na ƙasa kuma tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba; Associate Professor Sule Ya’u Sule; Inuwa Waya; da Hon. Kabiru Alhassan Rurum, wanda Babban Daraktan Hukumar National Productiɓity Commission, Hon. Baffa Babba ɗan Agundi, ya wakilta. Sauran sun haɗa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, da tsohon ɗan majalisar wakilai na Kano Municipal, Hon. Sha’aban Sharada.
Hakazalika, an bai wa mambobin da suka samu ɗaukaka lambobin yabo, ciki har da Babajide Otitoju, Jaafar Jaafar mai wallafa Daily Nigerian, Associate Professor Rukaya Aliyu, da Kwamared Ibrahim Garba Shuaibu, Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Kano. An kuma karrama wasu tsofaffin shugabanni da mambobi da suka samu ɗaukaka, irin su Lamara Garba Azare, Yakubu Musa, Abdulaziz Abdulaziz, Tajuddeen Suleiman, Osa Director, Aminu Ahmed Garko, da Edwin Olofu.
ƙungiyar ta kuma karrama gogaggun ‘yan jarida da lambobin dogon hidima, domin nuna godiya ga jajircewarsu a sana’ar, ciki har da Abdullahi Mallam Yusuf, Mohammed Kabir Ya’u, Mohammed Abdulsalam, Jacob Ajakaiye, Desmond Mbogh, Maduabuchi Jerry, da Ahmed Mohammed Soron Dinki.
Taron ya kammala cikin farin ciki, inda mahalarta suka bayyana shi a matsayin gagarumin biki da ya dace da martabar aikin jarida, hidima, haɗin kai da kwarewa a cikin Wakilan Jaridu na NUJ a Kano.
