Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu tara suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa.
Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Alhamis, 25 ga Disamba, 2025, a ƙauyen Bagewu da ke ƙaramar Hukumar Ringim ta jihar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar a ranar Alhamis. Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin ya shafi wata jajayen mota ƙirar ɓolkswagen Golf 3 mai lambar rajista LNG 983 ɗA daga Jos.
A cewar ’yan sanda, wani mutum ɗan shekara 45 daga ƙauyen Randawa da ke ƙaramar Hukumar Mani ta Jihar Katsina ne ke tuƙin motar. An ce motar ta cika da fasinjoji fiye da ƙima, inda take ɗauke da mutane 20, ciki har da maza shida, mata takwas da yara shida.
Rahoton ya ce motar tana tafiya ne daga ƙauyen Masaka da ke ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Dutsi a ƙaramar Hukumar Mani ta Jihar Katsina, lokacin da hatsarin ya faru.
Binciken farko-farko na ’yan sanda ya nuna cewa tayar gaba ta motar ce ta fashe tana tafiya, lamarin da ya sa direban ya rasa ikon sarrafa ta. Sakamakon haka, motar ta afka cikin wata bishiya da ke bakin hanya.
SP. Adam ya ce, fasinjoji 11 sun mutu nan take, yayin da sauran mutum tara, ciki har da direban, suka samu raunuka daban-daban. An gaggauta kai waɗanda suka jikkata asibiti mafi kusa domin samun kulawar gaggawa, kuma a halin yanzu suna samun sauƙi ƙarƙashin kulawar likitoci.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa ta fara cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin, tare da gargadin direbobi da su guji gudun wuce gona da iri da kuma cika motoci fiye da kima.
Sanarwar ta kuma jaddada muhimmancin duba lafiyar ababen hawa kafin fara tafiya, tare da nuna cewa duk wanda aka kama yana karya dokokin zirga-zirga zai fuskanci hukunci bisa doka.
A baya-bayan nan, yawaitar haɗurra a manyan hanyoyin Nijeriya na ci gaba da tayar da hankula, inda Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa, FRSC, ke alaƙanta mafi yawan su da gudu, shan barasa yayin tuƙi da kuma sakacin direbobi.
