‘Yan Majalisar Wakilai uku daga Katsina sun koma APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis ne ‘yan Majalisar Wakilai guda uku daga Jihar Katsina suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sun bayyana rikici na tsawon lokaci da aka gagara warwarewa da gazawar shugabanci a matsayin dalilan ficewarsu daga jam’iyyar.

‘Yan majalisar sune Salisu Yusuf Majigiri mai wakiltar mazabar Mashi/Dutsi da Aliyu Iliyasu Ruma na mazabar Batsari/Safana/Danmusa da kuma Abdullahi Balarabe Dabai da ke wakiltar mazabar Bakori da Danja, wadanda suka bayyana matakin nasu a sakonni mabanbanta, kamar yadda Kakakin majalisar, Tajudeen Abba ya fada a yayin zaman majalisar.

Hakan ya faru ne kwanaki shida da wasu takwarorinsu daga Jihar Delta suka koma APC daga jam’iyyar, yayin da wasu biyu daga Enugu kuma suka fice daga LP zuwa PDP.

Hakan ya nuna yadda APC ke cigaba da samun karin mambobi a majalisar da ma kasa baki daya duba da yadda sauye-sauyen jam’iyya ya zama zuwan dare acikin yan siyasa a matakin jihohi da kasa.

By Babaji