A kwanakin baya ne Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan yadda jihar ke rasa wasu yankunanta sakamakon hare-haren ƙungiyar Boko Haram a baya-bayan nan.
Gargaɗin nasa ya biyo bayan yawaitar hare-haren da ‘yan ta’addan ke kai wa a kullum a kan wuraren sojoji da na farar hula, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji da sauran al’umma a jihar Borno.
A makonnin baya-bayan nan ma, wasu da ake zargi ‘yan ƙungiyar ta Boko Haram sun kashe sojojin Nijeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar – a hari da suka kai Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala.
A baya dai gwamnatin Nijeriya ta ayyana cewa an fatattaki ‘yan Boko Haram, a lokacin gwamnatin Buhari. Wannan gwamnatin ta yi ikirarin cewa ƙungiyar ta ragu sosai ta yadda ba za ta iya fuskantar sojoji kai tsaye ba, sai dai ta kai hari a wurare masu rauni.
Abin baƙin ciki, ba a nan gizo ke saƙa ba. Hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan a jihar Borno, ba wai batun tsaro ba ne kawai, babban gargaɗi ne cewa kwanciyar hankalin da aka samu ta hanyar sadaukarwar sojoji na shekaru na iya rugujewa. Maganar da Gwamna Zulum ya yi a lokacin wani taron tsaro na gaggawa a Maiduguri ya nuna wani lamari mai cike da ruɗani: Boko Haram da ISWAP suna sake taruwa, suna ba da makamai, da kuma tabbatar da kansu a yankunan da sojojin Nijeriya suka ƙwato a baya.
Wannan sake ɓullowar ba ƙaramar illa ba ce ga gwamnatin jihar da ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sake tsugunar da dubban ‘yan jihar da rikicin ‘yan tada ƙayar baya sama da shekaru goma da rabi ya raba da muhallansu.
Ga yankin da ya shafe sama da shekaru 10 yana fuskantar ayyuka ta’addanci, alamun suna da ban tsoro. Hare-haren da aka kai kan sansanonin sojoji a Wajirko, Sabon Gari, Wulgo, da Izge, ya nuna yadda waɗannan gungun ‘yan tada ƙayar baya ke ƙaruwa sosai. Wani abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ake ganin raguwar aikin soja a fagen fuskantar wannan barazanar da ke ƙaruwa. Gwamna Zulum ya yi gargaɗin cewa, idan ba a kula da shi ba, zai iya warware nasarorin da aka samu na tsawon shekaru.
Tafkin Chadi – musamman Tumbus ya zama tungar ‘yan ta’addan bayan da sojojin Nijeriya suka yi gudun hijira daga dajin Sambisa da aka taɓa jin tsoro. Kiran Zulum na ayyuka soja na musamman a waɗannan tsibiran ba dabara ba ne kawai amma yana da muhimmanci. Wazannan yankuna masu nisa suna zama wuraren kiwo inda masu tsattsauran ra’ayi ke taruwa, suna koya musu, da kuma shirya sabbin hare-hare. Dole ne sojojin Nijeriya su ba da fifiko ga wazannan shiyyoyi idan ana so a ci gaba da samun nasara mai ma’ana ta tsaro.
Ya kamata al’ummar Nijeriya a matakin jihohi da na ƙasa baki ɗaya, su gane cewa wannan rikici ba gazawar tsaro ba ce kawai, kasawa ce ta siyasa. Misali haƙar ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba, ya zama wani aiki mai riba da ake gudanarwa akai-akai a ƙarƙashin kariyar jami’an rashawa da kuma hada-hadar jami’an tsaro. Lokacin da shugabannin siyasa da na gargajiya suka rufe ido ga waɗannan laifuka na tattalin arziki, suna ba da damar da ke haifar da ta’addanci.
Martanin gwamnatin tarayya na baya-bayan nan, ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar, abin yabawa ne. Alƙawuran ƙarin dakaru da kayan aiki, da kuma rahotannin halin da ake ciki na yau da kullum ga Shugaba Tinubu, ya nuna ɗaukar matakin gaggawa. Amma faɗa ba aiki ba ne. Dole ne ba wai kawai a ƙarfafa sojoji ba amma kuma a sake tsara su. Matsayin tsaro kawai ba zai wadatar ba. Dole ne a ci gaba da kai hare-hare tare da haɗin gwiwa, musamman a wurare masu zafi kamar Triangle Timbuktu da tsaunin Mandara, inda ‘yan ta’adda ke sake haɗuwa.
A matsayinmu na jarida, mun yi imanin miƙa wuya fiye da 300,000 na ‘yan tada ƙayar baya da iyalansu a cikin ‘yan shekarun nan, shaida ce ta tasirin hanyoyin da ake bi. Dole ne a ƙara ƙaimi, ba a Borno kaɗai ba, har ma a faɗin Arewa maso Gabas.
Bai kamata Nujeriya ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a Arewa maso Gabas da ma faɗin ƙasar.
Muna kira ga gwamnati mai ci da ta ɗauki kwakkwaran matakai. Wannan ba lokaci ba ne na maganganu kaɗai, sai dai na jajircewa, da yunƙurin kawar da Nijeriya daga barazanar Boko Haram gaba ɗaya.
