‘Yan majalisun tarayya su daina mara wa dokokin da za su ƙuntata wa rayuwar talaka – Ɗanpass

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yi kira ga ‘yan majalisun dattawa da na tarayyar ƙasar nan musamman na Arewa su daina yarda da amince wa duk wata doka da za a kawo domin ƙuntatawa rayuwar talakawa ta wuce.

ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ne ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida, ya ce dole gwamnoni da da ‘yan majalisu su sani ba a zaman lafiya da ƙuncin rayuwa da talauci kuma haraji da ake son ƙaƙabawa mutane ba abinda zai haifar sai ƙarin talauci.

Ya ce abin takaici idan aka daka ta ‘yan majalisun dattawa da na tarayya komai aka kai musu sai su bari ya wuce wannan a dage a cize a ga an kawo hankalin Gwamnati tarayya akan ta sassautawa jama’a.

Ya ce yanzu harkar kasuwanci na cikin wani hali bankuna suna rike kuɗaɗe basa yawo ba zaka je banki a baka tsabar kuɗi ba, hakan tawaya ce ga yan kasuwa sosai idan aka ce za a tafi a haka kuɗi sai dai a waya aikwai matsala.

ɗanpass ya kuma yaba wa Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf bisa matakai da yake ɗauka wajen kyautata cigaban al’ummar Kano ta zo ta amince da biyan sabon tsarin albashi na ma’aikata da kuma biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu wannan abu ne mai kyau.

Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ya ce suna fata a ƙoƙarin Gwamnatin Kano za ta duba ‘yan kasuwa ta ɗauki matakai domin tallafawa a farfaɗo da masana’antunmu da suka durƙushe domin su ci gaba da aiki domin masana’antu za su taimaka don bunƙasa tattalin arziƙi.

By ukarofi