
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar ƴan sanda a jihar Kwara ta ce ta yi nasarar ceto mutane 20 da aka yi garkuwa da su a hanyar Osi/Obbo Aiyegunle da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce tawagar rundunar tare da haɗin gwiwar ƴan bijilante da aka fi sani da ƴan banga suka gudanar da atsayen.
Ta ce, jami’an sun ceto baki ɗaya mutanen a raye yayin da aka garzaya da wasu mutum uku da ke ɗauke da raunuka asibiti domin ba su kula.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen da aka yi garkuwa da su, sun taso ne daga Kwara zuwa jihar Kogi a motoci uku inda ƴan bindigar suka yi garkuwa da su a ranar Juma’a.
Ta ƙara ba cewa, babu ɗaya daga cikin ƴan bindigar da aka yi nasarar kamawa.
