Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta sanar da daƙile yunƙurin garkuwa da mutane a Ƙanƙara tare da ceto fasinjoji 11 da aka sace a hanyar Sheme zuwa Ƙankara.
Haka kuma jami’an tsaron sun ƙwato shanu 25 da wasu ‘yan bindiga suka sace a Malumfashi bayan musayar wuta da maharan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an bisa jarumtaka da gaggawar ɗaukar mataki.
Ya yi kira ga alummar jihar da su taimakawa jami’an tsaro wajen bada bayanan sirri na maɓoyan waɗanan miyagun mutane.
Yan sanda a shirye suke su kare rayuka da dukiyar alummar jihar.
