EFCC ta cafke Saleh Mamman a Kaduna bayan kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 75

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta yi nasarar kama tsohon Ministan Wutar lantarki, Saleh Mamman bayan tsawon lokaci yana ɓuya.

Hakan na zuwa ne bayan kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari sakamakon samun sa da hannu a laifukan da suka shafi badaƙalar kuɗaɗe.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun cafke Mamman ne a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Talata.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ke gudana a hedikwatar hukumar.

A cewar Olukoyede, an samu nasarar kamo tsohon ministan ne bayan bincike da bibiyar da jami’an hukumar suka yi.

Ya bayyana cewa, da fari EFCC ta shigar da Mamman ƙara ne akan tuhumar sa da zargin sauya akalar sama da Naira biliyan 33 da aka ware don ayyukan wutar Mambilla da Zungeru.

A yanzu dai ana sa ran hukumar za ta fitar da ƙarin bayanai akan yadda aka kama shi da kuma matakan da za a ɗauka don tabbatar da cika ƙa’idojin doka akansa.

By Babaji