
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta ƙaddamar da bincike akan zargin mummunan farmaki a gidan wani mai suna Haruna Bashir a Unguwar Ɗorayi Charanchi Quarters, wanda ya yi ajalin Fatima Abubakar mai shekarun 35 da ‘ya’yanta shida.
A cewar sanarwar da Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa ya fitar, hukumar ta samu rahoton faruwar al’amarin da misalin ƙarfe 12:10 na ranar Asabar.
Kiyawa ya bayyana cewa, an farmaki waɗanda abin ya shafa ne da wasu muggan makamai da wasu ɓata gari ke ɗauke da su ta hanyar kutse a cikin gidan.
Ya ƙara da cewa, tuni Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya umarci tawagar jami’ai ƙarƙashin jagorancin Mataimakinsa na ɓangaren ayyuka, DCP Lawal Isa Mani zuwa wajen da iftila’in ya faru.
Daga lokacin ne aka garzaya da gawarwakin zuwa asibitin Murtala Mohammed inda a nan aka tabbatar da rasuwarsu.
Haka kuma, Kwamishinan ya umarci mataimakinsa na sashen binciken manyan laifuka (CID), ACP Wada Jarma da ya gudanar da bincike mai zurfi a kai tare da kamo masu hannu a ciki domin su fuskanci hukuncin doka.
A ƙarshe, rundunar ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da ɗaukacin al’ummar Ɗorayi Charanchi da ma jihar baki ɗaya.
