
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta musanta rahotannin da ke cewa ta karɓi wata takarda daga Gwamna Dauda Lawal na nema son shiga jam’iyyar.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa akwai zarge-zarge a jihar na cewa gwamnan na shirin komawa APC.
A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Yusuf Idris ya fitar ranar Asabar a Gusau, ya bayyana zargin a matsayin abin da aka ƙirƙira da ba shi da asali ko tushe.
A cewarsa, an ƙirƙiri zancen ne da nufin ruɗar da jama’a da ƙoƙarin haddasa rikici acikin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa, APC tana da kafafen da ta amince da su wajen yaɗa dukkan wani mataki da ta ɗauka yadda ya dace.
Ya ƙara da cewa, jam’iyyar ba ta samu kowane irin saƙo daga gwamnan ba kuma ba ta san ko akwai wani shiri daga gare shi da ya shafi ficewa daga PDP zuwa APC, yana mai kiran mambobin jam’iyyar musamman na Zamfara da su ƙaurace wa zancen.
