’Yan sandan Katsina sun kama Sahabi Rabi’u kan zargin kashe mace da jaririyarta

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

’Yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mai suna Sahabi Rabi’u da zargin kashe wata mata da jaririyarta. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu ya sanar da haka a wata takardar sanarwa.

Ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a garin Sheme da ke ƙaramar Hukumar Faskari, inda ake zargin Sahabi da abokinsa da ake nema ruwa a jallo suka kai matar wajen garin Sheme, inda suka kashe ita da jaririyarta.

Kamar yadda DSP ya ce tuni wanda ake zargi ya amsa laifinsa ya kuma tabbatar da shi da abokinsa ne suka aikata wannan ɓarna.

Marigayiyar ‘yar shekara 30 kuma ‘yar asalin garin Sheme da ba a daɗi sunan ta ba sun samu saɓani na ‘yan uwantaka wanda ya kai ga Sahabi na aikata wannan ɓarna.

DSP Abubakar Sadiƙ ya bayyana cewa a halin yanzu Sahabi wanda ake zargi yana hannun ‘yan sanda a yayin da yan sanda sun shiga farautar abokinsa.

Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun gano gawar matar da jaririyar kuma ana gudanar da bincike.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Bello Shehu na jihar Katsina ya nuna takaicinsa bisa irin wannan rashin imani da wanda ake zargi ya aikata.

CP Bello ya tabbatar wa da cewa ‘yan sanda za su tabbatar da adalci a bincike da ta ke gudanarwa.

Kwamishinan ya yi kira ga mutanen yankin da ke da wani bayani da zai taimaka wa ‘yan sanda wajen kama abokin Sahabi ko kuma bayanai da zai taimaka a binciken da rundunar ‘yan sanda ke gudanarwa.

DSP Abubakar Sadiƙ ta tabbatar da cewa ‘yan sanda za su cigaba da bada bayanin halin da ake ciki da zaman ta samu wani sabon labari game da lamarin.

By ukarofi