Kisan Zariya: Za mu haɗu da Buhari ranar lahira – El-Zakzaky

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, waɗanda aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai fuskanci tambayoyi a gaban Allah Ranar ƙiyama kan kisan 2015 da aka yi wa mambobin harkar a Zariya, wanda ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mabiyansa.

Yayin taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Laraba, El-Zakzaky ya kuma zargi gwamnatin yanzu da karya alƙawarin da ta yi tun kafin ta hau mulki — wanda ya haɗa da biyan diyyar asarar rayuka da dukiyoyi, da kuma fayyace matsayar gwamnati kan harin.

Da aka tambaye shi ko ya yafe wa Buhari, El-Zakzaky ya amsa da cewa, “Ya riga ya mutu. Za mu haɗu a Ranar ƙiyama. Lokacin da nake cikin jini, ministan sa ya kira ni. Na ce masa ina jiran jinina ya ƙare ne na mutu, kuma ya miƙa gaisuwata ga Buhari. Na ce, za mu haɗu a Ranar ƙiyama.”

Ya ce, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati sun ziyarce shi kafin su hau mulki, inda suka yi alƙawarin shiga tsakani a lamarin. Sai dai ya ce tun bayan da suka hau mulki, babu abin da aka ce, balle a yi.

El-Zakzaky ya yi zargin cewa ana ci gaba da tauye haƙƙin bil’adama a ƙasar nan — ciki har da hana ’yancin taro da ’yancin faɗin albarkacin baki, yana misalta yadda ake murƙushe zanga-zangar ’Yan Shi’a ko ta Falasɗinu a gida da waje.

A cewarsa, “Masu mulki suna ganin suna da ikon yin yadda suka ga dama. Su karya haƙƙin mutane, su yi shiru tamkar babu abin da ya faru.”

Jogoran ya kuma danganta matsalar tsaro ta ƙasar da abin da ya kira “hannun gwamnati”, yana cewa, “Za su iya kawo ƙarshen rashin tsaro idan suna so.”

Yayin da ake shirye-shiryen tunawa da cikar shekaru 10 da harin Zariya, El-Zakzaky ya ce za a gudanar da baje-kolin hotuna da bidiyo domin tunatar da duniya abin da ya faru da kuma mutanen da suka rasa rayukansu.

Ya jaddada cewa ba za a iya murƙushe harkar da bindiga ko ƙarfin gwamnati ba, yana cewa, “Ba za ka kashe aƙida da ƙwaƙwalwa da bindiga ba. Muna magana, muna rubutu, kuma mutane suna karɓa. Ba za ka tsoratar da mu da bindiga ba.”

A cewarsa, harkar za ta ci gaba da tabbatar da ƙarfinta — na aƙida da na yawan mabiya — tare da neman adalcI, tantance abin da ya faru, da kuma neman alhakin hukuma kan kisan 2015.

By ukarofi