Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa al’umma cewa sauran ɗalibai da malaman makarantar St. Mary’s Catholic, Papiri, da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Agwara, Jihar Neja, za a kuɓutar da su cikin ƙanƙanin lokaci tare da mayar da su hannun iyalansu lafiya.
Wannan tabbaci ya fito ne daga bakin Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, yayin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, a Minna ranar Laraba domin jajanta wa jihar bisa harin.
Tun farko, an riga an ceto ɗalibai 100 daga cikin 259 da aka sace, inda Gwamna Bago ya karɓe su a ranar Litinin kafin daga bisani a haɗa su da iyalansu a Papiri ranar Laraba.
Minista Idris ya bayyana cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da ta’addanci, yana mai jaddada cewa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiki tuƙuru tare da jihohi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin ganin an dawo da sauran yaran da malamansu lafiya.”
Ya bayyana sace ɗaliban a matsayin wani abin girgiza al’umma, yana mai cewa samar da tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, “abu ne da ke buƙatar haɗin gwiwar kowa da kowa.”
A nasa ɓangaren, Gwamna Bago, ya jaddada muhimmancin kare dimokuraɗiyya da ciyar da ƙasa gaba cikin zaman lafiya da mutunta bambancin addini da al’ada. Ya yabawa gwamnatin tarayya bisa irin haɗin kan da take bai wa jihar wajen magance matsalolin tsaro.
